Main menu

Pages

YADDA ZAKI HADIN KANKANA DA MADARA. ( HADIN KASAITACCIYAR MACE)

 Yadda ake hadin kankana mai madara


A  yau zamu kawo muku yadda ake hadin kankana mai madara. Hadi Mai matukar muhimmanci ga Uwargida da Amarya ga hadin kankanan daki-daki:


Abubuwan hadawa

- Kankana

- Madarar gari

- Nutella

- Chocolate 


Yadda ake hadawa

Ki gyara kankana ki cire bakaken kwallayen da ke ciki sai ki yanka shi kanana ki ajiye a gefe.

Sai ki dauko plate ki jera kankanar a kai, sannan ki kawo garin madarar ki barbarda a kai.

Sai ki yaryada Nutella kuma sannan ki gutsura su chocolate na ki sai ki saka a kai. 

A sha dadi lafiya.
Karin bayani

Za ki iya markadawa idan baki sanshi a hakan. Za a iya duba girke girkenmu na baya don koyon wasu kalan abincin ko abin sha. Mai karatu ga misali: Yadda ake mixed fruits juice da kuma Yadda ake simple fruit salad da wasu dimbin abincin kala kala duk a wannan taska tamu.

Comments