Main menu

Pages

YADDA AKE HADA KANUNFARI DA MADARA DA AMFANIN DA YAKE A JIKI

 Yanda Ake Hada kanunfari da Madara da Kuma amfaninsa ga lafiyarmu.

Da yawa mutane suna neman magani ne, amma sai su tsallake asalin magani su tafi neman wani abu daban bisa rashin sani.


A yau insha Allahu zan sanar daku 2 daga cikin amfanin shan Garin kaninfari da madara ta ruwa ko nono


1. Yana magance matsalar saurin kawowa.

Matsalar saurin kawowa matsala ce da take damun mafi yawan magidan ta a wannan lokaci musamman ma wadan da basu da manyan shekaru, wanda hakan a tare dasu babbar illa ce da kuma barazana a zamantakewar su da abokan zaman su.2. Matsalar  infection.

Infection wanda aka fi kira da sanyin mara, shima yana daga cikin ciwukan dake damun jama'a mata da maza yan mata da zawarawa kai harda matasa.


Shin ta wacce hanya za a iya magance wadannan matsaloli da kaninfarin???


Za a nemi:

1. Garin kaninfari.

2. Madara ta ruwa/nono

Za a samu garin kaninfari rabin karamin chokali a zuba a ciki karamin kofi na madara ta ruwa ko nono a juya sosai sannan a sha, ana sha ne sau daya a rana na tsawon kwana 3 kacal.

Allah Yasa adace Ameen.

Comments