Main menu

Pages

TARIN FALALAR DAKE GA MAI YIN NAFILA

 



Falalar da Mai yin sallolin Nafila zai rabauta dasu a Lahira.


Daga; Mal. Dayyabu Umar Memai Rano. 


A Hadisin da aka karbo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) wanda Abu Dawud ya rawaito, Annabi (ﷺ) yace; "farkon abinda za'a yiwa mamaci hisabi dashi a ranar alkiyamah a ayyukansa shine Sallah, Allah Zai cewa mala'iku {Alhalin ya sani} “ku duba sallar bawana ya cikata ko ya tauyeta? Idan ta kasance cikakkiya sai a rubuta cikakkiya a gareshi.



 Idan wani abu ya tawaya sai Allah Yace ku duba ko bawana yanada sallar nafila, idan yanada sallar nafila sai Allah Yace ku cikawa bawan sallolinsa na farilla da sallarsa ta nafila”sannan a karbi sallolin". 



Mu sani ana karba fa Aljannah zaka tafi, kuma da temakon sallarka ta nafila. Idan hakane me hankali baze yarda ya dinga wasa da sallolin nafila ba. 

Allah Ya datar damu dukkan Alkhairi.


Comments