Main menu

Pages

SHEIKH TIJJANI GURUNTUM YAYI BAYANIN YADDA'YAN BINDIGA SUKA TARESU

 



Sheikh Tijjani Guruntum,yayi cikakken bayanin yadda'yan Ta'adda suka tsaresu

A yau ne labarin ya kewane kafafen sada zumunta na cewa yan ta’addan da ake tsammanin boko haram ko yan bindiga suka tare  Sheikh Ahmed Tijjani Guruntum tare da tagawarsu wanda tabbas abun ya faru ga yadda abun ya faru daga bakin shehin malamin.



Kamar yadda yan uwa suka gani yanzu nan a shigowar mu garin bauchi daga jamhuriyar Nijar saboda yadda abubuwa suka yadu a cikin al’umma wadansu hakane wadansu ba haka bane da kuma yadda wasu suke yada abubuwa masu tashin hankali wanda shima ya zama wajibi dole muyiwa yan 'uwa bayyani a taƙaice abinda ya faru abinda yake shine gaskiyar magana.



Kwanaki ukku da suka wuce mun tafi jamhuriyar nijar domin gabatar da wasu darusa na addini to jiya muka kammala darussan da dare yau kuma cikin taimakon Allah muka fito. Gaskiya ne 'yan bindiga sun tare mu da safiyar yau to bayan fitowar mu muna kan hanya tare da sauran malamai da muka tafi da su gaba daya , sai suka kewaye mu da bindigoginsu akan hanya suka tsare mu, so lokacin da suka tsare mu abinda suka fara yin kokarin yi a lokacin shine bude kofar motar.



To da yake central lock ne bazai buduba sai a cikin motar mu bude motar ko su bude mata wuta to bamu bude motar ba saboda duk mun dai dai ba zamu bude motar ba,  muna cikin wannan cece kuce daya daga cikin motocin da suke cikin tawagarmu ta baya malam sagir yana ciki, motar alhaji gwani to sai suka juya to daman duk kofar rago ne sun so dukka motaocin su shigo ne, to ganin wacan motar zata juya sai su kayi kanta da harbin bindiga cikin taimakon Allah juyawar tasu, sai direban mu ya hankalta da hankalinsu ya koma can shi kuma sai ya zaburi motar mu.



Cikin taimakon Allah dukka Allah ya kubutar da mu ba wadda aka ma rauni ba wadda akama kwarzane ba wanda wani abu ya same shi, akwai wasu bayin Allah wanda su ba a cikin tawagar mu suke ba to sai suka shigo cikin attack din harbin ya same su ciki mutum biyu wanda labari ya iske mu ba wani rauni suka ji ba.


Ga cikakken Bidiyon jawabin malam nan ku saurara.



Comments