Main menu

Pages

QUEEN ELIZABETH TA MUTU DA YAMMACIN YAU

 Sarauniyar England, Queen Elizabeth ta mutu a Yau.

Sarauniya Elizabeth ta biyu, wacce ita ce mafi daɗewa a tarihin ƙasar Burtaniya, ta mutu.

Elizabeth ta mutu tana da shekaru 96 a duniya.


Sarauniyar ta mutu cikin lumana a fadarta da yammacin yau,” in ji fadar Buckingham, a cikin wata sanarwa da yammacin yau Alhamis. “Sarki da Sarauniya Consort za su kasance a Balmoral a yammacin yau kuma za su koma London gobe.”Mijin Sarauniyar, Yarima Philip, ya riga ta rasuwa, wanda ya rasu a ranar 9 ga Afrilu, 2021, yana da shekaru 99 a duniya.Sarauniya Elizabeth ta bar ‘ya’yanta maza uku, Yarima Charles, Andrew da Edward; da kuma mace, Gimbiya Anne; jikoki Yarima William da Harry na Wales, Gimbiya Beatrice da Eugenie na York, da Peter da Zara Phillips, da kuma Lady Louise Windsor da James, Viscount Severn. Ta kuma rasu ta bar jikoki 12.

Comments