Main menu

Pages

NANKARWA, ABUBUWAN DAKE KAWO TA DA YANDA ZA A MAGANCETA

 Maganin Nankarwa da bubuwan da ke kawo ta (Stretch marks).

Nankarwa wasu  layukane marasa kyau gani da suke fitowa a jikin dan adam mace ko na miji wurare kamar su;-

Ciki daga kasa ko, mara ko, Saman mama ko, duwawu ko, Cinya dadi sauransu sassan jiki


       

Abubuwan da ke kawo Nankarwa

1. Daukan ciki zuwa haihuwa

2. yin kiba tashi guda 

3. Yin rama tashi guda

4. gado daga mahaifiya

5. damuwa mai yawa da makamantar su.

6. Jinya na tsawon lokaci

7. Shafa mayukan saken fada daga baka zuwa fara tas.

 

              

Yanda za a hada maganin Nankarwa

Asamu man zaitun da man ridi da man habbatus sauda da man kadanya, duk yawansu ya zama daya sai ahadasu waje guda agarwaya.

Arika shafawa bayan anyi wanka safe da dare, har awarke.

Allah Ya sa a dace

Comments