Main menu

Pages

AN CAFKE WANI MUTUM DA YA SIYAR DA DIYARSA MILLION 20

 



Yanda aka Kwamushe wani mutum da ya Siyar da diyarsa Million 20.


Wata babbar kotun yanki a Makurdin jihar Binuwai ta bayar da umarnin tsare wani mutum da aka gurfanar a gabanta a bisa kokarin sayar da ’yar cikinsa kan Naira miliyan 20.



’Yan sanda ne suka gurfanar da mutumin da abokinsa, bisa zarginsu da laifukan hadin baki domin aikata laifi da satar mutum da kuma safarar mutane.



Yan sanda mai gabatar da kara, Veronica Shaage, ta sanar da kotun cewa an kama wadanda ake zargin ne a kokarinsu na sayar da wata yarinya mai shekara hudu kan Naira miliyan 20.



lokacin da suke tsaka da kulla cinikin ne da wani mai suna Terna, ’yan sanda suka far musu, a inda wadanda ake zargin suka shiga hannu, shi kuma Terna ya cika wandonsa da iska.



Veronica ta karato sassa daban-daban na dokokin fenal kod na jihar, da masu laifin suka karya, ta kuma roki kotun da ta zartar musu da hukuncin da ya dace.



Alkalin Kotun, Dooshima Ikpambese, ta yi watsi da ikikarin masu karar na hurumin kotun na sauraron shari’ar.



Sannan ta aika da su gidan gyaran hali domin a ci gaba da tsare su har zuwa ranar daya ga watan Disamba a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraron kara. (NAN)



Wata kotu a Makurdi, Jihar Binuwai, ta ba da umarnin tsare wani magidanci mai shekaru 45, bisa zargin sayar da ’yarsa mai shekaru hudu kan Naira miliyan 20.



’Yan Sanda sun kamo mahaifin yarinyar ne tare da abokinsa, bisa zarginsu da aikata laifin hadin baki da sata da safarar karamar yarinya.



Alkalin kotun dai ta ba da umarnin tsare su a gidan kaso na Makurdin, tare da dage sauraren karar zuwa ranar 1 ga watan Disamba.


Tun da farko ’yar Sanda mai gabatar da kara, Insfekta Veronica Shaagee, ta ce sakamakon rahoton sirri da suka samu ne suka kamo mutanen, aka tsare su a sashen binciken manyan laifuka da ke Makurdi.


An dai kama magidancin da abokinsa ne suna tsaka da cinikin yarinar, sai dai wanda ake zargin zai saye ta ya cika wandonsa da iska.


Laifin da Shaagee ta ce ya sabawa sashe na 97 na kundin Penal Code na Jihar Binuwai na 2004, da sashe na 3(2) na dokar hana satar dan Adam na 2017, da na 2006 19 (1).

Comments