Main menu

Pages

HANYOYI BIYAR DA ZAKU BI DON MAGANCE BASUR KO WANE IRI NE




Hanyoyi Guda Biyar (5) na warkar da ciwon basir kowane Irine Insha Allah


Idan kana dauke da cutar basir, kuma baka son kashe kudi akan aikin tiyata, toh ka gwada bin wadannan hanyoyin Insha Allah za a dace.

 Suna aiki matuka sosai cikin yardan Allah.



 Alamomin da ke nuna Mutum na dauke da cutar basir:

Mutum zai rika fama da wadannan matsaloli kamar haka; 

- Kaikayi da bacin rai.

- Fitar jini, amma ba tare da anji zafi ba 

- Ciwon jiki da rashin sakewa 

- Kumburar dubura

 - Fitan curi ko dunkule a dubura Abubuwan dake kawo basir suna da dama, amma dai duk asalin su guda. 


Amma mafi yawancin sanadin basir sune: 

- Haihuwa

- Kiba 

- Fitan bayan gida da kyar 

- Yawan cin abinci mai maiko

Dayan ciki Wadannan hanyoyin na kawar da kamuwa da cutar basir, koma wani iri ne.


 1. Cin abinci mai gina jiki; Ana son mutum dinga cin kayan hatsi da kayan marmari da kuma ganyayyake don sune masu wanke tumbi kuma suna taimakawa wajen nika abinci a cikin ciki.

 - Suna kawar da wahalar yin bayan gida.

- Sannan sai su kawar da alamun basir.


Bugu da kari ana so mutum ya rage cin nau’in abinci mai maiko da kuma jan nama.


2. Yawaita shan ruwa mai kyau, domin yana wanke hanji kuma yana taimakawa wajen nika abinci a ciki. 


3. Yawan ci da shan sinadari bitamin C Sinadarin Bitamin C na kara wa jijiyoyi karko da lafiya. 


Don haka nau’o’in abinci irin su lemun tsami, tuffa da timatir na taimakawa wajen magance basir. 

Ya kamata kowa ya ringa yin wannan, har a masu juna biyu. 


4. Motsa Jiki. Yawan zaman dabano ba tare da motsa jiki ba na janyo wahalan tsuguno.


 - Motsa jiki na taimakawa wajen baiwa jijiyoyi da ciki kansa koshin lafiya.


 - Motsa a jiki a kullum zai magance matsalar cutar basir.


5. Wanka da ruwan dumi Idan kana bukatan kawar da alamun basir kamar su ciwon jiki da kaikayi, toh kayi wanka da ruwan dumi hadi da ganyayyaki. 


- Hakan zai saukar da ciwon jikin kuma ya tsaida kaikayin. 

- Kuma zai hana kumburi.


MAGANIN BASUR:

Idan basir yayi tsiro, Ana samu danya ( zait lauz /namijin goro)  a kwaba shi da danyan kwai, a dinga turawa a cikin dubura, yana kashe basir mai tsiro kuma yana konar da basir da ya toshe dubura.



HADIN MAGANIN BASIR NA BIYU:

GANYEN AYABA :

zaka dafa kana shan Kofi daya da safe da yamma.

Sanna zaka zauna cikin ruwan ganyen ayaba tsawon minutes 10.


MAGANIN BASIR NA UKU:

A samu ganyen riyhan busasshe sai a daka shi yayi laushi sannan a samu man zaitun ko habbatussauda sai a kwaba a rinka cusawa ta dubura.

Za a yi haka sau biyar a yini daya.


A samu shibtu a rinka hadawa da Zuma ana sha a kuma rage kadan a rinka cusawa a dubura.


A dinga shan habbatussauda safe da yamma Ko zuma da man zaitun Suna magani basir.


A samu za'afaran a daka shi a hada shi da kwaiduwar kwai egg danye a rinka sha safe da yamma.


A samu wadannan mahadan

■ citta

■ tafarnuwa

Sai a daka su waje daya a rinka dibar cokali daya ana hadawa da Zuma Ana sha sau daya safe da yamma.


da yawa mutane suna kasa banbancewa meye basir, da yawa mutum daga yaji cikinsa yana kugi ko yana ciwo sai yace basir yana damunsa, amma da yawa wasu cututtuka suna kama da basir kuma yana cutarwa da yawa.


Yakan sa sha'awar mutum ta bangaren jima'I ta dauke, ya kansa ciwon ulcer domin yana hana cin abinci, yana kuma kawo wata cuta wadda ake ce wa (sha'awatul kaziba),shine mutum daya fara cin abinci sai yaji ya koshi.


Kowa da kowa zai iya samun wannan matsala ta Basir, maza da mata.


Amma ba a cika ganinsa ga yara ba, an fi ganinsa ga manya, Kuma kowa zai iya samunsa a kalla sau daya a rayuwarsa.


A manyan ma sai masu nauyi sosai, kamar mutane masu kiba.


A mata za a ga basir ya fi yawa a lokacin da mace ta samu juna biyu saboda nauyin da ta kara yayin daukar ciki, Idan ta haihu kuma ya baje.

 

Allah Ya sa a dace Ameen.

Don Allah duk Wanda ya karanta post din nan ya tura ma wasu a matsayin sadaka.

Comments