Main menu

Pages

AMSOSHI HUDU DA MUTUM ZE AMSA KAFIN YA WUCE ALJANNAH.

 Amsoshi hudu da kowane Musulmi sai ya amsa su kafin ya wuce Aljannah


Daga:

Mal. Dayyabu Umar Memai Rano. 

 

Annabi (ﷺ) yace: "duga-dugin dan Adam bazasu gushe ba se anyi masa tambayoyi hudu a ranar lahira. Ta daya za'a tambayeshi akan rayuwarsa, a ina ya karar da ita. Se ta biyu za'a tambayeshi iliminsa me yayi dashi ta uku, dukiyarsa a ina ya nemota kuma a ina ya kasheta, sannan se tambaya ta hudu jikinsa a ina ya tsufar dashi. Inde kaga mutum ya wuce lafiya ya tafi Aljannah to amsa ya bayar ta wadannan tambayoyi wacce ta gamsar da Allah subahanahu wata'ala. Ya Allah ka bamu ikon yin rayuwa yadda Allah yakeso Ka bamu ikon yin aiki da iliminmu ka bamu ikon duba ta ina dukiyarmu zata shigo mana, kuma ta ina zamu kasheta, sannan Ka bamu ikon tafiyar da jikinmu ta hanyar bin Allah yadda tsufansa ze zamo ya gudana saboda Allah. 


Comments