Main menu

Pages

YADDA ILLAR BILICIN YA MAYAR DA 'YAR 22 YEARS KAMAR TSOHUWA

 


Illar da bleaching yayi ma wata yarinya ta zama kamar tsohuwa

Wata matashiya mai suna Ellen ta bayyana irin halin tasku da ta shiga saboda yunƙurin da ta yi na sauya launin fatarta.


Matashiyar mai shekara 22 ta ce duk da ta yi nasarar sauya launin fatar tata cikin sauri, bilicin ya tsofar da ita kuma ta zama kamar 'yar shekara 40.


Kazalika, ta ce lamarin ya saka ta ta ji kamar an kulle fatarta ne a gidan yari saboda matsalolin da ta fuskanta a lokacin da ta yi yunƙurin daina shafe-shafen.


Dole Ellen ta koma launin fatarta na asali don ta yi maganin ƙuraje da tabo-tabo da suka cika mata fuska.

To dama ance duk Wanda ya raina tsayuwar wata to ya hau sama ya gyara idan har zai iya. Ina kira ga 'yan uwana Musulmai da mu guji aikata ire iren wadannan abubuwan, don yanzu saboda masifa ma wai har namiji ma sai kaga yana bleaching, to Allah Ya kyauta Ya shiryemu baki daya.

Comments