Main menu

Pages

MU LEKA KITCHEN (KOSAN DOYA MAI KIFI)
 Yadda  Ake Kosan Doya Mai Kifi

Doya 1/2

Kwai 1

Cornflakes 1 sachet

 Maggi 1

Gishiri Rabin cokali karami

Sukari Rabin cokali karami

Kifin gwangwani

Mai cokali daya

Alayyahu cikin hannu daya

4 Attaruhu

1 Albasa

cokali Curry karamin

cokali Mayan kamshi karamin


HADAWA:

Zaki fere doya ki yankata kanana kisa gishiri da sukari ki dafata.

In ta dahu sai ki marmasa ta sosae tayi laushi.


Ki yanka albasa ki jajjaga attaruhu ki zuba a kaskon suya ki soyasu sannan ki zuba kifin gwangwani ki juya kisa kayan kamshi da maggi ki zuba alayyahun da kika wanke kika yanka. Ki soyasu na Minti 3 ki kashe.


Sai ki rika dibar doyar kina fadadashi sannan ki zuba hadin kifin da kikayi ki dunkulashi yayi kamar ball.


Ki fasa kwai ki kadashi ki rika tsomawa aciki sannan kisa a dakakken cornflakes kina soyawa a mai.


     

Comments