Main menu

Pages

  


Yadda Ake yin Dambun Kifi

➡kifi mai kyau

➡attarugu da albasa

➡kayan kamshi

➡maggi da gishirih

➡mai

Da farko zaki wanke kifinki da ruwan khal ko ruwan tsami sai ki gyarashi sosai ki fitar da dattin jikinshi sai kisa a tukunya kisa kayan kamshinki dasu maggi tafarnuwa da sauransu saiki daura a wuta kamar zakiyi silalen nama, ruwa kadan za kisa saiki barshi yadan dahu kadan ki kwashe. Idan yasha iska saiki nema turminki kisaka ki daka shi ya daku yanda kikeso saiki kwashe ki ajiye agefe saiki daka attarugunki da albasa saiki hada da kifin ki gyauraya su sosai saiki kawo kayan kamshinki dasu magginki kisa hadasu akai sai ki jujjuya suhade jikinsu sosai saiki daura kaskonki kisa mai kadan kiringa soyawa.


Kifi

Maggi

Attaruhu

Albasa

Kayan kamshi

Zaki wanke kifinki bayan ya tsane sai a zuba a tukunya adan sa ruwa kadan a yanka albasa da maggi yadan turara kadan saiki sauke adakeshi a turmi da su attaruhun a soya.


Amna tunda kifine sai Nike ga ba sai an daka a turmi ba, kina iya matmadheshi da hannunki tunda ba karfine dashi kamar nama ba. Kina iya samun hand gloves kisa sai ki marmashe saboda gudun Karni kar ya bata miki hannu.Comments