Main menu

Pages

KO KUNSAN MATSALOLI BIYAR DA TSADAR MAN DIZEL YA HAIFAR A NIGERIA

 


Matsaloli guda biyar da tsadar man dizel ya kawo a Nigeria 

Harkokin yau da kullum na daidaikun mutane masu sana’o’i da kamfanoni da ma gwamnati na cikin matsanancin hali a Najeriya sakamakon tsadar dizel — kuma hakan na shafar masu amfani da kayayyaki da ayyuka a kowane mataki na rayuwa.


Kasancewar an dogara ga dizel a harkar sufuri da ma harkoki da dama, wannan matsala ta tsadar man, wanda galibi manyan motoci ke amfani da shi sannan kuma ake amfani da shi wajen samar da lantarki a ma’aikatu da masana’antu ya sa ake fama da tsadar rayuwa da kuma dakatar ko takaita wasu harkokin na gwamnati da ‘yan kasuwa.


A kwanakin baya ne dai kungiyar masu samar da albarkatun mai da iskar gas (NOGASA) ta yi gargadin cewa farashin dizel din zai iya kaiwa Naira 1,500 daga Naira 800 idan ba a dauki mataki ba.


Wannan kuwa kungiyar ta ce zai kasance ne a sakamakon  kalubalen da masu shigo da shi ke fuskanta.



BBC ta yi nazari kan wasu matsaloli da tsadar man na dizel ta haifar a Najeriya zuwa yanzu, lamarin da ya shafi rayuwar jama’a da gudanarwar kasuwanci da ayyukan gwamnati.


Masana’antu

Kungiyar masu masana’antu a jihar Kano ta ce sama da kashi 50 cikin 100 na masana’antu da ke aiki a jihar sun dakatar da aiki sakamakon tashin farashin dizel da kuma karancinsa.


A hira da BBC kungiyar ta ce tana fargabar in dai aka ci gaba da samun karanci da tsadar man su ma masana’antun da suka rage wadanda ke aiki a yanzu ka iya rufewa baki daya, inda hakan ka iya tilasta wa da dama daga cikin wasu masana’antu a Kanon fara sallamar ma’aikatansu.


Tuni dai wasu ma’aikatan a sassan Najeriya da ma jihar ta Kano wadanda suka rage tsawon lokacin ayyukansu ko kuma ma suka rufe suka sallami wasu daga cikin ma’aikatansu.


Wannan ya jefa rayuwar irin wadannan ma’aikata da iyalansu cikin mawuyacin hali kasancewar wasu da wannan aiki kawai daman suka dogara.


Masu injin nikan hatsi 

 Injin nikan hatsi na daga fannin da talakawa masu karamin karfi yawanci suka dogara da shi wajen samar da abinci mai dan sauki, inda sukan kai nikan masara da gero da makamantansu wadanda ake sarrafawa wajen yin nau'ukan ci-maka.


Kuma masu wannan sana'a ta nika sun dogara ne kacokan ga man dizil wajen tafiyar da wannan sana'a ta su, wadda yawanci a yankuna na karkara da ma birane a unguwanni na masu karamin karfi ake yi.


Wani mai sana'ar nikan da BBC ta tattauna da shi a Kano, ya ce sakamakon tsadar man na gas a yanzu yawancin abokan sana'arsa sun daina aiki.


Saboda wadansu daga cikinsu ba injinansu ba ne, suna bayar da balans ne sannan su biya ma'aikatan da suke tare da su suma kuma su samu nasu.


Mutumin ya ce a kullum yana sayen lita 10 ta man da yake aiki da shi zuwa magariba, a kan Naira 8300.


Wato kowa ce lita yana ta man yana sayenta a kan Naira 830, wadda a baya ya ce suna saye a kan naira dari biyu da wani abu zuwa dari uku.


Ya ce a kan ba sa so dole suka kara kudin nika, wanda a baya suke nikan kwano daya a kan Naira 20 zuwa 30 yanzu suna yi a kan Naira 50 zuwa 70, abin da ya sa kasuwarsu ta ragu.


Wasu suka daina ma sana'ar, ma'aikatan da suke aiki da su sun fada kangi na rashin abin yi.


Manyan motocin dako da sufuri

Wani direban babbar motar dakon mai da ke zirga-zirga daga arewacin Najeriya zuwa kudu, musamman jihar Lagos, mai suna Danjuma Fagge ya shaida wa BBC, irin halin fargabar da suke ciki.


Ya ce akwai abokanan aikinsu da ke aiki a wani kamfani da tuni suka rasa ayyukansu.


“Suna aiki ne karkashin wani dan kasuwa da ke da manyan motocin tirela da tankuna har 11, amma yanzu ya sanya motocin gaba daya a kasuwa, saboda ba riba a sanadiyyar tsadar man motar,” in ji shi.


Direban ya kara da cewa shi kansa a duk tafiyar da zai yi daga Kano zuwa Lagos a yanzu ana ba shi kudin mai sama da Naira miliyan daya da dubu dari uku.


Ya ce ''A yanzu kusan kashi 35 cikin 100 na masu harkar motocin dakon musamman masu dauko mai sun tsaya.''


Harkar gine-gine

Wani mai sana'ar sayar da yashi a Kano da BBC ta ji ta bakinsa dangane da yadda sana'ar take a halin yanzu, ganin cewa harka ce da ita ma ta dogara ga motocin da ke amfani da man na dizel, ya ce suma lamarin bai bar su a baya ba.


Ya ce motar tifa ta tsakiya da suke sayar da yashinta mai tsakuwa Naira 18,000 a yanzu ta koma Naira 28,000, wato karin dubu goma.


''Shi kuwa yashi mai laushi wanda a da ake sayar wa Naira dubu tara zuwa goma, ko a jiya naira dubu goma sha takwas muka sayar,'' in ji shi.


Ita ma kasuwar rodi na gine-gine ta tashi inda rodin da ake sayarwa a da Naira 2300 yanzu ya koma Naira 3400.


Sai dai kuma wani mai sana'ar sayar da siminti ya ce, akwai saukin tashin farashi a kan siminti, idan aka yi la'akari da yadda farashin sauarn abubuwa ke tashi.


Ya ce '' Ina ganin watakila saboda motocin kamfani ne ke sufurin shi ya sa.''


A yanzu dai ana sayar da buhun simintin dangote a kan naira dubu hudu a hannun yawanci manyan 'yan kasuwa a Kano.


Bankuna

Kasancewar yawancin bankuna su ke samar da lantarkin da suke tafiytar da harkokinsu ta hanyar amfani da manyan injinan da ke amfani da man na dizel, wanda kuma sakamakon tsadarsa da lalacewar hanyar samar da lantarki ta kasar, wannan yasa bankuna da dama suka rage lokacin hada-hadarsu.


Wasu bankunan ma rahotanni na nuna cewa sun dakatar da ayyukan wasu rassansu a Najeriyar a sanadiyyar tadar man na gas.


Bayanai na nuna cewa rassan wasu bankuna suna budewa ne daga karfe 8 na safe zuwa 1 na rana ko 2 ko 3 ko ma karfe 4 na yamma.


Lokacin ya dogara ne ga bankin da kuma inda reshen nasa yake.


Gidajen rediyo

Bayanai da BBC ta tattaro sun nuna cewa wasu gidajen rediyo musamman na 'yan kasuwa tsadar man na dizel kan sa har su dakatar ayyukansu a wani lokaci saboda ba za su iya sayen man da za su yi aiki ba, bisa la'akari da cinikin da suke yi da kuma dawainiyar da ke kansu ta tafiyarwa da kuma biyan ma'aikata.



Hatta wasu gidajen rediyon mallakar gwamnatoci kan dakatar da ayyukansu a duk lokacin da babu wuta da suke samu daga kafar lantarki ta kasar.


Saboda ba su da mai ko halin da za su iya samar wa kansu man na dizel da za su yi aiki.


Wasu tashoshin kuwa bayanai sun nuna suna rage tsawon lokacin gudanar da ayyukansu ne.


Ita dai wannan matsala ta tsada da karancin man gas na dizel a watan Maris na wannan shekara 2022 Nairametrics, kafar da ke bayar da rahotanni da bayanai da fashin baki kan harkokin kasuwanci ta yi rahoton cewa duniya za ta iya fuskantar karancin man dizil saboda takunkumin da ake sanya wa rasha.


Wanda ake fargabar hakan zai shafi kasashe matalauta kama daga najeriya zuwa Sri Lanka, wadanda ke sayen man dizil din na Rasha.


Rahoton ya nuna cewa za a samu gibin ganga miliyan uku a duk rana a kasuwar duniya saboda takunkumin da aka dora wa Rasha.


Akwai dai fargabar cewa al'amura za su iya kara ta'azzara mudddin yanayin farashin man bai yi sauki ba a kasuwar duniya, abin da ke da alaka da yakin da Rasha take yi da Ukraine, wanda ya janyo wasu manyan kasashen duniya suka sanya mata takunkumi, lamarin da ya janyo tsadar rayuwa a kusan duk duniya.

Comments