Main menu

Pages

KUNUN SHINKAFA DA AYA DA KWAKWA

 


Kunun Shinkafa da Aya da Kwakwa

Assalamu alaikum Warahmatullah
Yau mun zo maku da Wani hadin kunun Shinkafa da Aya da kuma Kwakwa. Ga yadda akeyi;


Ingredients

Shinkafar tuwo cup 2

Aya cup 1

Kwakwa Kwallo daya

Fresh milk

1/2 cup condensed milk

Ruwa dai dai Bukata.


Yadda za a hada;

Da farko zaki jiqa shinkafar da aya na tsahon 2hrs ko ki jiqa su da daddare su kwana idan kika tashi seki goga kwakwa don tayi saukin nikawa sekisa a blender da cups of water kiyi blending har sai yayi laushi.Sai ki juye a roba ki zuba 3cups na ruwa akai kisa matachi ki tace sai ki dora a wuta on a medium heat kina juyawa a hankaliZakiyita juyawa har sai yayi kauri sosai sai ki kawo fresh milk ki dinga zubawa kina juyawa har sai kin samu dai dai yadda kike son kaurin seki zuba condensed milk ko sugar seki sauke


Asha da dumi nayi garnishing da coconut flakes.

Comments