Main menu

Pages

KO KUNSAN CEWA ADAM ZANGO BAI TABA ZUWA SAUDIYYA BA, YA FADI DALILIN SA
Adam Zango ya Fadi dalilin sa na rashin Zuwa Saudiyya aikin Hajj ko Umrah


Assalamu alaikum Warahmatullah

Turkashi babbar magana hakika wasu sunce Adam a zango ya tashi daga jarumi ya koma rago daga jin wannan kalmar daya fada kasan jarumin yana da tsoro matuka domin har yanzu baya yarda yayi doguwar tafiya acikin jirgin sama.Wannan Bama shi kadai ba akwai mutane da yawa wa’yanda basa kaunar hawa jirgin sama saboda fargaba wasu kuma jiri da faduwar gaba kowa dai akwai nasa dalilin kuma baka hana kowaba saboda dalilan kashin kaiA wannan hajjin da akayi na bana anjiyo surutan mutane akan cewa meya hanashi zuwa domin sauke farali ganin cewa bai taba Zuwa yin aikin Hajjin ko Umrah ba, Kuma anyi Shekara biyu ba ayi aikin Hajj ba sai a bana, Shekara ta uku kenan.To anyi Zaton zai hanzarta cikin mahalarta wannan kasa don sauke nauyin falralin dake kansa. To sai dai yayi burus da mutane sai a wannan lokacin sannan yayi bayaniYa fadawa Duniya cewa shifa saboda tsanani tsoron da yakewa jirgin sama ne shi yasa har yanzu ya kasa zuwa domin yin aikin hajji amma yace lokaci yananan zuwa da Allah zai nufeshi daya sauke wannan faralin. Hakika mutane sunyi mamaki dajin wannan kalaman daga bakin jarumi adam a zango domin duk a zaton wasu ya jajje wannan gari na Makka ashe dai be taba zuwa ba to muna yi masa fatan Allah ya nufeshi da zuwa dan ba a ce kudine matsalar shiba.

Karin bayani a cikin wannan Video
Comments