Main menu

Pages

KANNYWOOD SUNYI MARTANI AKAN HANA SU YIM AMFANI DA KAYAN POLICE A FILM

 


Martanin da wasu directors na Film suka mayarwa sufeton 'yan sanda

Umarnin da Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriya ya bayar ga masu shirya fina-finai su daina amfani da kayan sarki na 'yan-sanda da kuma daina muzanta aikin dan-sanda a shirye-shiyensu na talabijin, ko zane ba tare da izinin rundunar ba, ya ja hankalin masu sana'ar.


A umarnin Usman Baba ya ce daga yanzu rundunar ba za ta amince da yadda ake amfani da kayan-sarki da sauran abubuwa na ‘yan-sanda ba a fina-finai, ba tare da izini ba kamar yadda doka ta tanadar.


Ya ce idan ba haka ba to kuwa duk wanda ya karya doka zai ɗanɗana kudarsa.


Sanarwa da kakakin rundunar na kasa CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce "kada wani mai shirya fina-finai da ya sake nuna ‘yan-sanda a matsayin marasa kirki ba tare da izini ba a rubuce daga rundunar yan-sanda."



Sanarwar ta ƙara da cewa ba za ta amince da bayyana aikin ɗan-sanda ba a fina-finai, matsawar abin da aka kwaikwaya a aikin ba shi da kyakkyawan tasiri ga al'umma.


Masu shirya fina-finai a Najeriya kan kwaikwayi jami'an ‘yan-sandan kasar, kuma a mafi yawan lokaci ba a nuna su a mutanen kirki.


Wannan lamari ya janyo masu harkar fina-finan Hausar na Kannywood magana.


Martanin wasu daraktocin Kannywood

Wasu daga cikin masu harkar fim din Hausa na Kannywood wadanda wannan umarni na ‘yan-sanda ya shafi aikinsu na mayar da martani.


Aminu Saira, fitaccen mai bayar da umarni ne a fina-finan Kannywood, kuma ya shaida wa BBC cewa za su duba su gani idan umarnin na Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriyar yana kan doka za su kiyaye.




Idan kuma suka duba suka ga su ma abin da suke yi yana kan doka to za su hada kai da abokan aikinsu na Kudancin Najeriya su kalubalanci umarnin a kotu, in ji shi.

"Domin da mu da su duk doka ce ta kirkire mu a Najeriya."


Ya kara da cewa "Duk wanda yake zaune a kasar nan da jami’in gwamnati da wanda ake mulka da mai mulki da ko waye suna karkashin doka ne.’’


"Saboda haka idan doka ta kasa ta haramta mana mu nuna kayan ‘yan-sanda kuma mu yi amfani da su a cikin fim dole za mu girmama dokar kasa kuma mu hakura ba yadda za mu yi,’’ in ji daraktan.


A cewarsa: "Amma idan doka ta ba mu dama to za mu yi yaki batun iya iyawarmu, iya karfinmu da mu da na Kudu da na Arewa mu hadu idan ya so ita dokar kasa ta fito ta fassara cewa haramun ne mu yi amfani da shi ko kuma a’a ba haramun ba ne kuna da dama ku yi amfani da shi.’’


Ya ce za su yi hakan ne domin kotu ta fayyace abin da doka ta ce a game da abubuwan da suke yi a fim kan ‘yan-sandan.


Daraktan ya kara da cewa su daman duk abin da suke yi a kan doka suke yinsa sai sun samu izini.


Ya ce akwai matsaloli da abubuwa da suka faru a baya wanda har Kwamishinan ‘yan-sanda ya fito aka yi maganganu a baya, wanda a lokacin aka ce duk wanda zai yi abin da ya shafi ‘yan-sanda sai ya samu izini.


"A yanzu maganar da nake maka akwai kamfani guda wanda aikinsa ke nan wanda da yardarsa da amincewarsa su hukumar ‘yansa dan ce ta ba shi lasisin duk wanda yake son wani abu na fim ko bindiga ko yunifom (uniform) ko wani abu ya tura musu sikirift din su za su duba su ga ni su za su nema masa famit (permit) daga wurin hukumar ‘yan-sanda,’’ in ji shi.

Daraktan ya ce tun daga wannan lokaci suke bin wannan tsari.


 Aminu S. Bono, wanda shi ma darakta ne a harkar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, ya ce yana ganin akwai kamar rashi ko karancin tuntuba daga bangaren Babban Sufeton 'yan-sandan.


 Ya ce yana ganin bai tuntubi hukumar shirya fina-finai ta Najeriya, domin a duk duniya a cewarsa babu yadda za a yi wata doka da za ta takaita wa mai wasan kwaikwayo amfani da wani abu kamar kayan lauya ko sojoji ko na asibiti ko wani abu domin abu ne da zai iya faruwa a zahiri.


Kuma hanya ce da ake nuna wa duniya kamar yadda kowace kasa take da tsarinta na aiki da suturar da ‘yan-sandanta da sauransu ke sawa.


Darektan ya ce kusan a duk fina-finan da suke yi akwai izinin ‘yan-sanda.


"Kamar mu a nan Jihar kano akwai difatment (department) guda wanda shi kwamishinan ‘yan-sanda ya bada wanda za a bi karkashi jagorancin PPRO, wanda suu ne ma wani zibin da kansu suke zuwa gurin da ake daukar fina-finan suke nuna ga yadda za a yi ga kuma yadda za a yi,’’ in ji shi.


Daratkan ya ce, "Kusan har fina-finai ma mun yi wadanda suka shafi ‘yan-sanda kai-tsaye wanda an yi amfani hatta police hedikwata ta Jihar Kano na yi amfani da ita kuma an yi amfani da abubuwa da yawa.’’


Ya ce daga irin fina-finan da suka yi akwai irin su "Kwana Casa’in akwai ‘Barazana’ da sauransu, wadanda aka yi ta aiki kafada da kafada da ‘yan-sanda.


Ya kara da cewa ba ma sa amfani da kayan ‘yan-sandan a yanzu sai dai wanda aka ba su, domin akwai wadanda suke da izinin hukumar ‘yan-sandan a Kannywood suke samar da kayan.


Kuma sakamakon matsalolin da ake samu kamar sanya kayan ‘yan-sanda ba daidai ba da sauran matsaloli ya sa aka kirkiri kujera ta musamman ta wakilcin hukumar ‘yan-sanda da sauran bangarorin al’umma a hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano.


Dangane da wannan doka ko umarnin na Babban Sufeton ‘yan-sandan yana ganin abu ne da zai sake nazari a kai idan ya zauna da wadanda abin ya shafa za a gyara.


Inda ya bayar da misalin wasu dokoki ko umarnin da ‘yan-sandan ke bayarwa a baya daga bisani su sauya matsaya bayan sun yi nazari

Comments