Main menu

Pages

DABARUN TARA (9), NA YIN AMFANI DA TUMATUR.



Dabarun Yadda Zaki amfani da Tumatur


1. Idan za ki yi jar miya ki yi amfani da tumatir masu dan tsaho kuma jajaye sun fi dadin miya, zagayayyun tumatir tsami ne da su musamman a cikin miya.



2. Idan za ki nika kayan miya ki tabbatar ki yanka tumatir din gida biyu kin cire tsakiyar ko kuma kin matse ruwan da yake ciki domin rage tsami a cikin miya



3. Idan za ki yi miya ki dafa tumatir har sai ruwan tumatir din ya kone, musamman idan tumatir din da yawa kuma kina so ki ajiye shi na wani lokaci.



4. Idan tumatir ya yi yawa a cikin miya kuma ya cika tsami kina iya saka ‘yar kanwa kadan ko kuma bakar hoda(baking powder)



5. Tumatir mai kyau za ki gan shi ja kuma babu wani baki a jikin shi, babu kwarzane ,idan da akwai dan baki a jikin shi to karshenta wani gefe daga ciki ba shi da kyau


 

6. Idan tumatir mai kyau ne idan kin matsa shi za ki ji yana da dan taurinsa, ba da kin matsa shi ba ya lagutse ruwa ya fito. Idan kin ga wani wuri ya fara lobawa a jikin tumatir to ya kusa lalacewa ki yi sauri ki yanke wurin ki yi amfani da shi



7. Idan za ki sayi tumatir da yawa to kada ki sayi nunannu, ki sayi wanda basu karasa nuna ba. Idan kin tashi amfani da shi kuma bai karasa nuna ba sai ki saka tumatir a cikin takarda da ayaba, to zai nuna nan da nan.



8. Kina iya sayen danyen tumatir wato korensa ki ajiye shi a wajen da ba haske zai ringa nuna a hankali



9. Kanshin tumatir yana iya tabbatar da kyawaunsa da kuma dandanonsa.


Comments