Main menu

Pages

HANYOYIN DA ZAKI BI DON RAGE TUMBI

 Hanyoyin da Za kibi don rage Tunbi.


Assalamu alaikum Warahmatullah
A yau mun kawo maku yadda zakuyi ku rage katon tumbi idan kina dashi.kowane lokaci anfi so aga Cikin Mace a shade, kamar ma ace ba 'yan hanji, in dai har ba ciki gareta ba. Don haka ga yadda zakuyi.

• Lemon tsami 

• Citta danye 

• Tafarnuwa(idan kina so)

• Zuma 


Yadda Zaki hada

Sai ki goga ko markada lemon tsami, citta da tafarnuwa, idan kin gama sai ki juye a tukunya kisa ruwa kofi daya ki tafasa su.


idan kin tafasa sai ki barshi yayi sanyi ki tace sai ki sa zuma ki sha.

Yana da kyau kisha kafin ki kwanta barci

na tsawon kwana 7


NOTE

Mai ciki ko shayarwa kar ta sha wannan hadin.

Sai dai ta tafasa ganyen tsamiya idan yayi sanyi sai ta sa zuma ta sha.


Mai fama da rikicewar al'ada idan tasha Al'adar ta zai iya zuwa a ranan ko washe gari. Kuma yana maganin infection


Don Allah ku turawa wasu

Comments