Main menu

Pages




Hadin Kasaitacciyar Mace, Gyara da kanki


Assalamu alaikum Warahmatullah 
Yau mun zo maku da wasu sirraka na Karin Ni'ima ga Mace, da abubuwan da zatai amfani dasu wajen inganta kanta.

1- Ruwan Abarba: Yana da kyau mace ta rinka markadawa tana tacewa tana sha da sugar ko zuma, wannan hadin yana karawa mata Ni'ima sosai da sosai.


2. Rakke: Shima yana karawa mace ni’ima kuma yana da amfani matuka a jiki, domin Yana karawa Macce Ruwa.


3. Aya: ita ma duk tafiyar su daya da rake, ayar anaso irin bula bulanan tana da matukar muhimmanci gurin mace tana da ni’ima sosai, kuma za'a iya samun kunun aya a hada shi da madarar peak ta ruwa.


4. Zaitun: Man zaitun yana magunguna da yawa to anaso macce ta ringa shafashi ajikinta yana gyara fata da saka santsi jiki, hakama yanada kyau macce ta dinga shafawa a gabanta, yana saka laushi.


5. Bawon bagaruwa: ita kuma wani sirri ne wanda idan mace na son ta zama kullum a tsuke ta dinga dafa bawon ta na shiga kamar yanda ake shiga ruwan dumi idan an haihu.


6. Ga kuma wani hadi a nemi sasaken baure, kananfari, zuma, citta, mazarkwaila. Za ki tafasa sasaken baure ya dahu sosai sai ki daka kanumfari me yawa da citta yar kadan ki zuba akai, ki saka mazarkwailan da zuma amma zaki cire icen kafin ki zuba hadin, sai ki sauke ki dinga sha daidai kima idan ya huce, wannan hadin kadai ya ishi macce, ba sai ta wahalda kanta neman boka ko wani asiri tana raba kanta da Allah ba.


7. A samu zogale a wanke shi a nika shi tare da dabino da kuma kwakwa sai a tace a saka zuma tare da madara sai a saka ya yi sanyi a rika sha bayan mangariba.


8. Wannan hadin yana kara ruwa, Ruwan kwakwa ,Nikakken ridi, Garin dabino,Madara ta ruwa a hada su guri guda a dama miji zai sha mace ma zata sha, Yana karawa Oga Kuzari, kuma yanasa Nushadi.


9. Ina mata masu fama da matsalar bushewar gaba? ki samu man ridi ki rinka zubawa cikin ruwan dumi ki zauna a ciki, sannan ki rika matsi da Albabunaj ko Hulba.

Comments