Main menu

Pages

GASKIYAR MAGANA DAGA BAKIN ADAM ZANGO AKAN ZUWAN SHI SAUDIYYA

 Gaskiyar magana da Adamu Zango kan Zuwa kasar saudiyya.


Assalamu alaikum Warahmatullah. Na zo maku da Wani posting Kuma akan Adam Zango, game da zuwansa kasa Mai tsarki. Wasu daga cikinmu Basu da fahimta. Dazun munyi posting akan cewa Zango bai taba Zuwa Makkah sauke farali ba.Ba anyi posting din bane don cin zarafi ga shi Adamun ba, sai don mahanga guda biyu. Ta farko kamar yadda wasu masu fahimta sukai ta mashi addu'a Allah Ya bashi ikon zuwa ba a San bakin wa Allah Zai karba ba, sai kuga Allah Ya cire Mai tsoron jirgin ya samu Zuwa.Saboda ba rashin kudi, ba rashin Lafiya, ba rashin kyawun hanya, kawai ra'ayin shi na baya kaunar jirgin sama da shi shaidan ya samu damar katange shi daga wancan babban rabo.Sai muyi fatan Allah Ya sa Yana cikin wadanda suka amsa Kiran Annabi Ibrahim A.S. Abu na biyu Kuma shine yadda celebreties suka mayar da Saudiyya kamar gida, Hajj da Umrah kullum a hanya suke, to Shima Muna fatan Allah Ya bashi wannan ikon.Saboda masu karyata post din dazun ga babbar hujja nazo maku da ita, na kawo maku cikakkiyar firar da akayi da Adam Zango, inda a cikin firan ne ya furta cewan cikin kasashen da yake burin Zuwa Saudiyya na ciki Amma rashin son jirgin sama yasa baije ba, Amma yana sa rai nan gaba.Ga Video ku kalla. Idan baza ka iya kallo daga farko har karshe ba, to ka wuce Minti 7:20, wato Minti bakwai da sakan ashirin daga nan tambayar ta fara, inda akace kasashe nawa yaje anan zakuji amsar da ya bayar. 


Ga video, Minti 7;20, daga nan bayanin ya fara.

Comments