Main menu

Pages

BABBAR MAGANA, ILLAR DA RASHIN CIN NAMA KE HAIFARWA MACE. - BINCIKEN MASANA

 Matan da ba sa cin nama za su iya karyewa a kwankwaso - Bincike   

 

 Assalamu alaikum Warahmatullah

Masana kimiyya sun yi nazari kan abinci da mata masu shekaru 35 zuwa 69 suke ci

Matan da ba sa cin nama za su iya fuskantar yiwuwar karyewa a kwankwaso nan gaba a rayuwa, kamar yadda wani bincike ya nuna.Masu binciken sun rika bin rayuwar mata   26,000 na tsawon shekaru 20 kuma sun gano cewa  kashi daya bisa uku na matan da ke cikin rukuni da ba sa cin nama sai  kayan lambu ko kayan itace za su iya samun karaya ko targade fiye da masu cin nama.Kwararru daga Jami'ar Leeds sun ce wasu daga cikin matan da ba sa cin naman na iya rasa sinadaran inganta lafiyar kashi  da tsokar kashi lamarin da ke haifar da hadarin karaya.Sai dai duk da haka mawallafan rahoton sun ce bai kamata wadanda ba sa cin nama su yi watsi da cin kayan lambu da na itace ba.

Masu binciken sun yi nazari  a kan rukunin mata masu shekaru 35 zuwa 69 domin tantance alaka tsakanin lafiya da abinci. Kusan kashi 28 cikin 100 na matan da aka rika bin yadda suke rayuwa  wadanda ba sa cin nama ne, yayin da kashi daya cikin dari wadanda ba sa cin nama ne da madara da kwai da duk wani nau'in abinci da ake samu daga wurin dabobbi.


 

Masu bincike sun ce rashin cin abinci mai gina jiki na shafar lafiyar kashi da na tsokar kashi.

Jagoran binciken, James Webster, ya ce: "Bincikenmu ya nuna damuwa a kan hadarin samun karaya  ga matan da ba sa cin nama."Sai dai duk da haka kamar yadda yake game da kowane abinci, yana da muhimanci a fahimci yanayin mutum da kuma abinci mai gina jiki da ake bukata domin inganta lafiyar jiki."Mista Webster ya ce kayan lambu da na itace ba sa samar da abinci mai gina jiki irin su sinadarin Protein da Calcuim wadanda aka fi samunsu a nama fiye da ganyayyaki.


"Rashin samun wadannan abubuwan gina jiki zai iya samar da kashi mara kwari kuma yana shafar ingancin tsokar kashi wanda zai iya sa mutum cikin hadarin samun karaya a kugu," in ji shi.


 

Sai dai Mista Webster ya ce rashin cin nama ya bambanta daga mutum zuwa mutum kuma zai iya "inganta lafiya ko akasin haka", kamar sauran abinci da ake samu daga dabbobi.Su ma sauran masana kimiyya da ke cikin aikin sun ce mata za su iya kula da lafiyar kashi ta hanyar ganin cewa sun yi kokarin kaucewa rama, tare da cin abinci mai dauke da sinadarin B12 tare kuma da motsa jiki a-kai-a-kai.Dr Darren Greenwood ya ce "Wannan bincike wani bangare ne da ke nuni da yadda mata suke rayuwa idan tsufa da kuma abinci mai gina jiki da suke ci da lafiyar kashi da kuma tsokar kashi."Ana bukatar karin bincike domin sanin rawar da nauyin jiki ya ke takawa tare da gano dalilan da ke janyo haka a masu cin nama da masu cin kayan lambu da na itace.Ita ma Farfesa Janet Cade wadda tana cikin mawallafan rahoton ta ce binciken "na da muhimanci saboda zai bada damar fahimtar hadarin da ke tattare da masu cin kayan lambu na tsawon lokaci da kuma matakan da ya kamata a dauka domin kaucema haka."Masu binciken sun ce akwai bukatar gudanar da karin bincike domin tantance ko za a iya samun sakamako makamancin wannan tsakanin maza

Comments