Main menu

Pages

YANDA IYAYE ZASU HADA WAYARSU DA TA 'YA'YANSU DON KULA DA TARBIYYA

 


Yadda yadda Iyaye zasu hada wayoyinsu da ta 'ya'yansu.


Tun bayan da labari ya bayyana a watan Afirlu a shafin intanet cewa kananan yara daga makarantar Chrisland sun dauki kansu wani faifen bidiyo da waya, a yayin da ake cin zarafinsu ta hanyar lalata, ake ta samun martani kan yadda ya kamata mutane su yi don kare ƴaƴansu daga wannan lokaci na fasahar zamani.



BBC ta bi diddigin bayanan ƙwararru don samun shawarwarin da za su taimaka wa iyaye sa ido kan abubuwan da 'ƴa'ƴansu ke yi a cikin wayoyinsu na salula tare da kare su daga abubuwan da ke faruwa a shafin intanet.


Taiwo Ogunlade, wani mai yin sharhi a shafin Google, ya bayyana cewa sun ƙirƙiri wata manahaja da suke kira 'Family Link' don taimaka wa iyaye sa ido kan abubuwan da ƴaƴansu ke yi a shafin yanar gizo.


Lokacin da iyaye suka hada da wayoyin salularsu, za su iya toshe ko barin wasu abubuwa shiga cikin wayoyin salular 'ƴa'ƴansu.


Wannan zai sa iyayen su riƙa sanin abubuwan da 'ƴa'ƴansu ke kallo.


Za ku iya amfani da manahajar wajen toshe shafukan nuna faya-fayen bidiyon batsa da sauran abubuwan da ba su kamata ba.


Iyaye za su iya amfani da ita wajen sanin tsawon lokacin da 'ƴa'ƴan nasu suka shafe wajen amfani da wayoyin.


Hakan na nufin cewa iyayen za su iya kashe wayoyin salular ƴaƴan nasu a lokacin da wa’adin da aka daukar musu ya ƙare.


Yadda za ka iya hada wayar ɗanka da taka

1. Bude wa ɗanka shafin aika saƙonnin email na Gmail da shekarunsa na gaskiya.


2. Sauke manahajar Google Family Link a kan wayar salular iyaye.


3. Saka adireshin Gmail ɗin da ka yi wa ɗanka rijista da shi cikin manahajarka Google family link.


4. Yi amfani da sunan ɗanka na adireshin email ɗinsa wajen shiga cikin wayar salular, kana ka kunna. Wayar salularka za ta fara aiki tare da ta ɗanka.


5. Za su iya fara amfani da wayoyin, amma ba za su iya shiga cikin shafukan intanet da manya ke shiga da wayoyin nasu ba.


Ya kuma fitar da wasu shawarwari da za su taimaka wa iyaye sa ido kan sauran wayoyin ƴaƴan nasu. Sun hada da:


- Ajiye na’urar komfuta a daidai yadda za a ka iya ganin duk abubuwan da ke faruwa idan suna amfani da wayoyin salular.

- Ka riƙa taya su bincikar shafukan intanet a duk lokacin da suke buƙata.

- Kada ka riƙa bari a ko da yaushe suna yi su kadai.

- Ka toshe shafukan intanet ɗin da ba ka son si shiga.

- Kusan duka manahajoji na da ma’aikacin dannawa na toshe hanyar shigar.

- Ku tabbatar da saka lambobin sirri kana kada ku bari su bai wa wani.

- Ku riƙa magana da ƴaƴanku a ko da yaushe, kana ku ankarar da su cewa ka da su riƙa bai wa mutanen da suka haɗu da su a shafukan intanet bayanansu na sirri.



Shawarwari kan yadda za ku riƙa sa ido kan wayoyin ƴaƴanku

BBC ta tattauna da wata ƙwararriya a fannin al’amuran da suka shafi ƙananan yara, kana mai horarwa, Dakta Maymunah Kadiri, don yin karin haske kan abubuwa da dama da mutum zai iya sa ido kan ƴaƴansu da ke amfani da shafin intanet.


Dakta Maymunah wacce kuma ƙwararriya ce a fannin lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma gaɓoɓi, ta bayyana cewa da zarar ka sauke manahajar ta family link, za ku samu wata sanarwa da ke son shiga shafukan da ba su kamata ba, ta ce haka ta yi wa nata ƴaƴan.


Sauran shawarwarin da ta bayar sun ƙunshi:


- Saka kariyar yara a jikin talabijin da aka hada da tauraron dan adam. Da wannan, ba za su iya shiga tashohin da aka amince wa manya kadai ba.

- Ka saka kariyar kuma a shafin intanet dinka kamar su Netflix da YouTube.

- Ku rika kula da yadda suke samun damar shiga intanet din da kuma Wi-Fi.

- Ku saka makarantu su rika tantance suka wayoyin salular da yara ke zuwa da su makaranta, musamman wadanda ke zaune a dakunan kwana na makaranta.

- Ku rika sa ido kan abubuwan da ƴaƴanku ke yi bayan an kwanta da tsakar dare, saboda wasun su kan shiga dakunansu da wayoyin salularsu kana su cigaba da amfani da su bayan kashe fitilu.

- Ku rika amfani da shafin nan na WhatsApp web wajen shiga cikin abubuwan da suke tattaunawa, wannan zai taimaka muku wajen sanin irin abokan da suke hulɗa da su.

'Shekaru 13 ne mafi dacewa yara su fara amfani da waya' 

Dakta Maymunah ta bayyana cewa shekarun da suka dace ga ƴaƴanku su fara riƙe wayoyin salula kuma karkashin sa idon iyaye su ne daga shekara 13.


Ya kamata iyaye da makarantu sun rika neman taimakon ƙwararru a fannin fasahar sadarwar zamani su rika dubawa tare da goge wasu abubuwa marasa amfani daga cikin wayoyin ƴaƴansu, saboda wasu daga cikinsu na saukewa tare da ɓoye wasu abubuwa marasa kyau a cikin wayoyin.


Wasu daga cikin abubuwan da yaran ke kallo, ko ji ko karantawa na haifar da wasu matakai na lalata ƙwaƙwalwa idan suka girma cikin haka.


Dr Maymunah ta bayyana cewa yara a wannan zamani suna da matukar basira, da son sanin abubuwa, su kan shiga shafin matambayi baya ɓata na Google su samu hanyoyin da za su iya karya lagon makullin kare yara daga shiga wasu shafukan intanet da ba su kamata ba.


Ta ce yaran za su iya nuna ɓacin ransu, amma su dage sosai.


Kamar yadda ta bayyana, makarantu ne ya kamata su samo hanyoyin sa ido kan wayoyin da ɗalibai ke zuwa da su zuwa makaranta.


Ta kuma ƙara da cewa wasu daga cikin su sun fi samun damar shiga cikin shafukan intanet marasa kyau a gare su a lokacin suna makaranta

Comments