Main menu

Pages

SAU NAWA YA KAMATA A DINGA CANZA BEDSHEET, A SATI KO A WATA


Saunawa ya kamata a dinga canza zanin gado. Muhawara

 Wasu za su iya tunanin haka a matsayin wani batun da bai kamata a tattauna a kai ba a bainar jama'a, amma abu ne da ya shafi kowa da kowa: Sau nawa ya kamata ku rika sauyawa da wanke zanen gadonku.


Bincike ya nuna cewa baki bai zo daya ba kan wannan batu, kana wani sabon bincike a kan mutane 2,250 a Birtaniya ya gano karin rarrabuwar kai.


Kusan rabin mazan da ba su da aure sun bayyana cewa ba sa wanke zannuwan shimfidarsu har na tsawon watanni hudu, a yayin da kashi 12 bisa dari suka bayyana cewa suna wanke su a lokacin da suka tuna - wanda ka iya zama lokaci mafi tsawo.


"Wannan ba tsari ne mai kyau ba," Dakta Lindsay Browning, wata kwararriya a fannin halayyar dan adam, kuma kwararriya a fannin barci, ta shaida wa gidan rediyon Radio 1 Newsbeat.


Matan da ba su da aure sun fi yawan sauya zanen gado, kashi 62 bisa dari daga cikinsu suna wanke zannuwan shimfidarsu a ko wane mako biyu, kana ma'aurata na ikirarin wanke nasu a ko wane mako uku, kamar yadda bayanan da aka tattara daga kamfanin sayar da kayan shimfida suka nuna.


Shin mene ne ya sa muke bukatar sauya zannuwangadonmu?

Domin karin bayani, Dakta Browning ta bayyana cewa ya kamata mu rika sauya zannuwan shimfidarmu sau daya a ko wane mako, ko kuma a ko wadanne makonni biyu.


Kiwon lafiya shi ne babban dalili, kana daya daga cikin dalilan shi ne zufa. Idan ka taba kokarin yin barci a lokacin yanayin tsananin zafi, za ka san yadda hakan ke da matukar wahala.


"Zufa kan shiga cikin zannuwan shimfida ta haddasa ba ma wari ba, har ma da datti mai danko," in ji Dakta Browning.



Ka yi tunanin tashi daga barci cikin yanayin farin-ciki kamar yadda wannan matar ke yi a cikin wannan hoto


Ta ce muna bukatar iska mai kyau don jin dadi a lokacin da muke barci - saboda lokaci ne da za mu samu runtsawa mai dadi.


Amma ba zufa ce kawai ya kamata mu yi tunani a kai ba, kwayoyin halittar matacciyar fatar da muke fitarwa a lokacin da muke barci su ma abin damuwa ne.



Idan ba ka wanke zanen gadonka a kai-a kai, kwayoyin halittar matacciyar fatarka za su dankare a jikin shimfidar."


Babu dadin ji? Yakan kara muni. Wannan dankarewar na nufin kananan halittu kamar su kwarkwata za su iya kiwo a kan wadannan kawayoyin halittu tare da haddasa kaikayi da kuma kuraje a fatar jiki.



Shin lokutan shekara ma abin dubawa ne?

Kusan haka.


"Za a iya yi mana uzuri kadan a lokacin watannin hunturu," Dakta Browning ta bayyana, amma sau daya a mako "zai fi dacewa."


Idan za ka kai fiye da ko wadanne mako biyu "kana shiga cikin wani wuri marar kyau ne."


Duk da cewa zufa kadan muke yi a lokacin hunturu, amma za mu cigaba da fitar da kwayoyin halittar matacciyar fata, in ji ta.


"Kana za ka kwanta barci da hannaye masu datti kadan, da kuma numfashin da ke fitowa daga bakinka."


Dakta Browning ta ce lokacin bazara na kara ta'azzara matsalar alaji na shakar burbushin furanni.


"Yana da matukar muhimmanci ka rika wanke zanen gadonka akai-akai saboda za ka iya samun wannan matsala ta alaji a kan gado, wanda zai sa ka samu irin wannan toshewar hanci." A bincike, kashi 18 bisa dari sun bayyana cewa yin wanka da dare, saboda kada zanen gadon ya yi datti, shi ne dalilin da ya sa ba sa yawan sauya kayan shimfidar.


Wurin hutawa da natsuwa

Mantuwa kashi 67 bisa dari (67%), wadanda ba su damu ban kashi 35 bisa dari (35%), kana wadanda ba su da wani wankakken zanen gado kashi 22 bisa dari (22%) su ne manyan dalilan da suka sa mutane ke cewa ba sa sauya zannuwan gadonsu sosai, a yayin da kashi 38 bisa dari ke cewa ba su amince cewa suna bukatar yawan wanke zannuwan shimfidarsu ba', kamar yadda binciken Pizuna Linens ya nuna.


Dakta Browning ta bayyana cewa ya kamata dakinka ya zama wani ''hutawa'' don yin barci, kana ''wuri mai kyau, da tsari inda za mu ji farin-ciki."


Tana da marasa lafiya da ke fama da matsaalar rashin barci kuma ta bayyana cewa "idan zannuwan gadonka ba a wanke suke ba, kana suna da datti, suna wari, yana kara irin wani yanayin cewa gadonka ba wuri ne da kake so ka kwanta ba."


"Idan muka kwanta a kan gado kana muka ji matsuwa, da dadi, da farin-ciki, kana sabon kamshin zanen gadon na taimaka mana samun nutsuwa da farin-ciki."

Comments