Main menu

Pages

MU LEKA KITCHEN (YADDA AKE SUYA (TSIRE))

 


Yadda Ake Hada hadadden Suya (Tsire) A gida

INGREDIENTS:

Nama,

borkono,

kuli-kuli,

citta,

kimba,

kanunfari,

masoro,

thyme,

curry,

busashen tafarnuwa 

da sauran spices.

Mangyada,

gishiri,

maggi sai tsinkin tsire.

.

PROCEDURE:

Ki daka dukkanin spices naki tare da kuli, amma kulin ya ďan fi yawa, kuma ki sanya maggi da gishiri. A zabi nama mai kyau wanda babu kitse sosai a jiki, sai ki yanka shi sirara ta kwance da dan tsayi kadan sai ki ďauko tsinken tseren ki jera wannan naman a jiki. Wato in kin huda ta ciki sai ki fitar da shi ta waje. Daga nan sai ki sami kwano ki zuba mangyada dai-dai misali tare da gishiri da maggi kaďan ki shafe jikin naman duka. Kina yi kina sanya shi cikin haďin kulin ya kama jikinsa da kyau. Daga nan in a oven ne sai ki yi ta jera su suna gasuwa. In ma a rushi ne duka ba damuwa. 


Comments