Main menu

Pages

 Yadda Ake Hada Gas Meat


Abubuwan da ake bukata

Jan nama, albasa ko lawashi, markadedden gyada, kori, thyme, tattara, attarugu, tumatur kadan,maggi, kabeji, in ana so citta, tafarnuwa, foil paper ko takardan cementi, da leda baki

    

Yadda ake yi

A wanke nama

A yanka albasa ko lawashi

A jajjaga tattara da attarugu

A yayyanka tumatur

A hada nama, albasa, da kayan miya, da gyada,kori, thyme, maggi da sauran kayan kamshi a gauraya, idan anaso a sa tumatur ko kuma a barshi sai bayan kori ya nuna a zubashi danye akan naman a ci.A juye had in baki daya acikin foil paper a kunshe ko kuma a leda, sai a sa ledar a cikin takarda, takardan kuwa a cikin wani leda.

A dora tukunya da ruwa, idan yayi zafi ko ya tafasa a dora matsami kamar za ayi dahuwar dambu, a dora kunshi akai a rufe da marfin tukunya a bari ya nuna.


Idan ya nuna za a iya garnishing da cabbage, tumatur, koren tatttasai a ci.

Za a iya kuma amfani da oven in da hali ba dole sai tukunya ba.

Comments