Main menu

Pages

MATSALAR DA OSINBANJO YA SAMU A KAFA HAR TA KAI ZA AYI TIYATA

 


Anyi admitting VP Osinbanjo a asibiti Jiya

Mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce, likitocinsa za su yi karin bayani a nan gaba.Wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na asali mallakar mataimakin shugaban kasar, ta nuna cewa za a yi wa Osinabjo tiyata saboda wani matsanincin ciwo da yake fama da shi a kafarsa.
“An kwantar da ni a asibiti a yau, inda aka min aiki, saboda wani ciwo da yake yawan damu na a kafa.Watakila sanadiyyar wasan kwallon squash na samu raunin.” Takaitacciyar sanarwa ta ce, wacce aka kafe ta da wani jan kwallo a shafin Facebook din mataimakin shugaban kasar a ranar Asabar.“Likitocinsa za su yi karin haske kan maganin da ake masa.” Akande ya ce a shafinsa na Twitter.
Sai dai sanarwar ba ta ambaci asibitin da aka kwantar da mataimakin shugaban kasar ba.


Osinbajo, mai shekaru 65, ya zama mataimakin shugaban kasa ne a shekarar 2015 bayan da suka lashe zabe tare da Shugaba Muhammadu Buhari.

Comments