Main menu

Pages

KO KINSAN SIRRIN DAKE CIKIN HADA MADARA DA ZUMA?

 Yadda Hadin Madara Da Zuma ke da Amfani A Lafiyar Jiki

Ki nemi zuma ki zuba a kofi ki sa madara a kai, ki gauraya ki shanye. Za ki ban labarin irin ni'imar da za ta saukar miki".


Wannan abu ne da za a ji a bakin mata da dama suna fada wa junansu, a matsayin wani sirri na saukar da ni'ima.To amma, da gaske yin hakan na saukar da ni'ima? Idan kuma yana saukarwa, to da zarar an sha zuma da madarar ne kawai sai ni'imar ta fara zuba? Ko kuwa sai an ɗauki wani lokaci ana sha sannan zai fara aiki?Abin da za mu duba ke nan a cikin wannan makala, duba da yadda mata da yawa suka yi amanna da lamarin, ba tare da la'akari da ko akwai wacce take da lalurar da bai ma kamata ta sha zuma ko madara ba, a tattaunawarmu da Maijidda Badamasi Shu'aibu Burji, kwarrariya kan nau'ukan abinci ko ci-maka mai gina jiki.Tarihi dai ya nuna cewa a ƙasashen Gabas ta Tsakiya akwai wasu jinsin mutane irinsu Indiya da 'yan Girka da al'ummarsu ke amfani da zuma a wajen aure, wanda daga nan ne aka samu kalmar "honeymoon" wato 'jin dadin rayuwa'.Haɗin zuma da Madara

Madara da zuma hadi ne mai karfi da ke taimaka wa lafiyar jiki, bayan gamsuwa ko taimaka wa mata wajen jin dadin jima'i.


Hada zuma da madara, na kuma taimaka wa mutum wajen samun bacci mai nutsuwa da lafiyar ƙarfin ƙashi da kuma inganta lafiyar zuciya, a cewar ƙwararru.Maijidda Badamasi Shu'aibu Burji ta shaida wa BBC cewa madarar shanu aka fi son ayi amfani da ita, saboda ita ke kunshe da dukkanin sinadarai da ake bukata masu inganci.Sannan idan za a sha hadin, ana son a dinga shan kofi guda na madarar shanu da zuma cokalin shan shayi guda, ana kuma son ake shansa da sanyin safiya kafin a ci komai.Abubuwan da haɗin ke yi a jiki

Shan zuma da madara a kullum na kara kuzari da saukar da ni'ima da inganta lafiyar maniyyi ga maza da kuma taimaka wa mata wajen saurin daukar ciki.Zuma tana kunshe da sinadarai masu dama da ke yakar cuttutuka a cikin jikin dan adam da kare lalacewar kayan halitta na haihuwa.


Haka kuma hadin zuma da madara na taimakawa wajen samun ingantaccen bacci, karfin kashi da lafiyar zuciya.


Madara ita kanta zalla na dauke da sinadarai calcium, wanda ke ƙara karfin kashi.


Shan zuma da safe da zarar an tashi daga bacci, tana bin jiki da bai wa jikin sinadarin cabohydrate mai kara karfin jiki.Sannan ita kuma madara zallarta na dauke da sinadarai irinsu protein a matakin farko, wanda ke taimakwa lafiyar jiki da kuma kuzari.


Daidaita ƙwayoyin halitta domin gamsuwa a jima'i

Zuma na daidaita kwayoyin halitta, wato hormonal imbalance, wanda shi ke sa a samu gamsuwa ta bangaren jima'a.Zuma na kuma daidaita lalurar nan ta mata wacce ke sa su kasance suna dauke da wasu nau'ukan na halitta maza da ke sa su samu gemu ko kiba ko rashin haila kan lokaci, to zuma na daidaita hakan.


Sannan an gargadi mata da ke sa zuma a cikin farjinsu da sunan samun dadin gasmuwar jima'a.


A cewar ƙwararru yin hakan ba ya komai sama da haifar da cutar kaikayin gaba wanda warkewarsa ke da wahalar gaske.Sanin lafiyar jiki

Kwararru dai na cewa zuma na ƙunshe da nau'ukan sukari iri daban-daban da a turance ake cewa "Complex sugar", don haka dole sai mutum ya kula ya tabbatar da yanayin lafiyar jikinsa kafin ya soma irin wannan hadi.


Malama Maijidda, ta ce duk da alfanun shan haɗin madara da zuma akwai mutanen da madara ke rudar da cikinsu, sannan akwai masu ciwon suga ko diabetes, da suma ba a son su yi wannan hadi.


Wannan dalili ya sa kwararru ke shawartar mutum ya san yanayin jikinsa, kafin ya tsiri shan zuma da madara, kar garin neman gira a rasa ido

Comments