Main menu

Pages

KO KINSAN ABUBUWAN DA KE KAWO CIWON BAYA GA MAI CIKI

 

 

Abubuwan da ke janyo ciwon baya ga mai ciki

Mata da dama ne ke fama da ciwon baya a yayin da suke da juna biyu kuma akwai dalilai da dama da ke janyo hakan, in ji likitoci.


Wasu daga cikin dalilai na zahiri sun hada da karin nauyi da mace ke yi a lokacin goyon ciki, inda jariri ke kara girma da ruwan da yake ciki shima yake kara yawa.



Haka kuma likitoci sun ce mata masu juna biyu kan kara kiba, wanda shi ma hakan yana daga cikin abubuwan da ka iya janyo musu ciwon baya.



Wasu karin dalilan da ke janyo mata masu ciki ciwon baya su ne idan mace na shan taba ko ta taba samun ciwon baya a da ko ta taba zubar da ciki.


Sannan idan mace tana dadewa ba ta yi jinin al'ada ba.

Haka kuma idan mace ba mai kazar-kazar ba ce kuma ta zo ba ta motsa jiki a lokacin da take da ciki shi ma hakan na iya janyo ciwon baya.


Hatta wasu ayyukan cikin gida na yau da kullum, kamar misali yadda mai juna biyu ke daukar abu mai nauyi shi ma yana da tasiri wajen janyo ciwon baya.


To domin jin yadda mai juna biyu za ta kiyaye yin wasu abubuwan da ke janyo ko ta'azzara ciwon baya, sai ku saurari hirar da Habiba Adamu ta yi da wata kwararriyar likitar mata da ke jihar kano, Dr. Iman Warshu, a cikin shirin lafiya zinariya na wannan makon.

Comments