Main menu

Pages

KAMANCECENIYAR DAKE TSAKANIN TUNUBU DA ATIKU

 Alakar kamanceceniyar da ke tsakanin Tunubu da Atiku

Wai Me Abin Gardama Akan Atiku Da Tinubu? Shin Akwai Bambanci A Tsakanin Su Ne? 


1. Tinubu na da mata kirista, Remi, Atiku ma ya taba auren mata Kirista, Jennifer. 

 

2. Tinubu na sallah akan kujera, Atiku ma na sallah akan kujera. 


3. Shekarun Tinubu 70 (b1952), shekarun Atiku 76 (b1946). 


4. Tinubu da Atiku duk asibitin kasashen waje suke zuwa. 


5. Tinubu da Atiku duk ba talakawa bane, masu kudi ne.  


6. Yayan Tinubu da na Atiku a kasashen waje suke karatu. 


7. Idan Tinubu yana da gida a kasar waje, to Atiku ma yana da shi. 


Don haka ba amfanin batanci ga waninsu don sun fi kusa da juna akan kai talaka mai kumfan-baki akansu.


Kawai kowa ya tabbatar ya yi zabe, amma da addu'ar Allah ya baiwa wanda shine mafi alheri gare mu duka, koda ba wanda mutum yake so ba ne!

Comments