Main menu

Pages
 Tarin Falalar Dake cikin yin Sallar Dare


Sallar Nafila Itace Sallar da Mutum keyi domin neman karin lada bayan Salloli biyar na farilla da aka wajabta masa daga cikin falalolin Sallar dare ita za ayi amfani da ita a cikama Mutum Farillarsa idan tasami rangwame. Acikin Sallolin nafila Sallah mafi falala itace Sallar nafila a cikin dare. kamar yadda yazo acikin wannan Hadisi:-An karbo Hadisi daga Abi Hurairata Allah Ya karamasa Yarda Yace:-Manzon Alla Tsira da Aminci Su Tabbata a gareshi Yace:-Mafificin Azumi bayan Azumin watan Ramadan shine Azumin Watan Al-Muharram mafificiyar Sallah bayan Sallar farilla itace Sallar dare Muslimu ya Ruwaito shi.Idan mukayi nazarin wannan Hadisi zamu ga daga cikin abubuwan da yake koyarwa akwai falalar Sallar nafila a cikin dare tareda fatan zamu kiyaye murika aikatawa gwargwadon iyawarmu

Comments