Main menu

Pages

FALALAR SALATIN ANNABI MUHAMMAD SAW

 



FALALAR SALATIN ANNABI (SAW) RANAR JUMA'A. 


ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ( ﺹ ) : ﻣَﻦ ﺻﻠّﻰ ﻋﻠﻲّ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ -

ﻣﺎﺋﺔ ﻣﺮﺓ - ﻗﻀﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻪ ﺳﺘﻴﻦ ﺣﺎﺟﺔ : ﻣﻨﻬﺎ ﻟﻠﺪﻧﻴﺎ ﺛﻼﺛﻮﻥ ﺣﺎﺟﺔ ، ﻭﺛﻼﺛﻮﻥ ﻟﺮﺟﻞ 


Ma'ana:

🌷Manzon Allah (SAW) ya ce: Duk wanda yayi Salati gare ni ranar Juma'a sau 100, Allah zai biya masa bukatun sa 60, Cikin su akwai bukatun duniya 30 da 30 bukatun Lahira.


🌷An rawaito daga Sheikh Suduq (rahimahullah) da

Isnadi zuwa Imam Muhammad Bakir (a.s): cewa An tambaye shi Menene mafificin aiki a ranar Juma'a? Sai yace: BAN SAN WANI AIKI DA YA FI SALATI GA MANZON ALLAH (SAW) DA ALAYENSA (A.S) BA.


🌷A wani hadisin Manzon Allah (saw) yace: "WANDA YA YI SALATI A GARENI RANAR JUMA'A SAU DARI (100) ALLAH ZAI GAFAR TA MASA ZUNUBAN SHEKARA TAMANIN".


🌷Salatin Annabi (saw) shine  mafi soyuwa a wajen Allah Ta ala.


ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ( ﺹ ) : ﻣَﻦ ﺻﻠّﻰ ﻋﻠﻲّ ﻣﺮﺓ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ

ﻋﻠﻴﻪ ﻋﺸﺮﺍً ، ﻭﻣَﻦ ﺻﻠّﻰ ﻋﻠﻲّ ﻋﺸﺮﺍً ﺻﻠّﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻣﺎﺋﺔ

ﻣﺮﺓ ، ﻭﻣَﻦ ﺻﻠّﻰ ﻋﻠﻲّ ﻣﺎﺋﺔ ﻣﺮﺓ ﺻﻠّﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﺃﻟﻒ ﻣﺮﺓ ، ﻭﻣَﻦ ﺻﻠّﻰ ﻋﻠﻲّ ﺃﻟﻒ ﻣﺮﺓ ﻻ ﻳﻌﺬﺑﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﺃﺑﺎ


Ma'ana:


🌷Manzon Allah (S) ya ce: Duk wanda yayi mun

Salati 1, Allah zaiyi masa 10, Wanda kuma yayi 10, Allah zaiyi masa 100, Wanda kuwa yayi 100, Allah zaiyi masa 1000, Sannan duk wanda yayi 1000, Allah bazai Azabtar dashi da wuta ba har bada.


ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ( ﺹ ) : ﻣَﻦ ﺻﻠّﻰ ﻋﻠﻲّ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏٍ ، ﻟﻢ ﺗﺰﻝ

ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﺗﺴﺘﻐﻔﺮ ﻟﻪ ﻣﺎ ﺩﺍﻡ ﺍﺳﻤﻲ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ


Ma'ana:

🌷Manzon Allah (Saw): Duk wanda Yayi Salati gare ni cikin Littafi, Mala'iku basu gushe ba Suna nema masa gafara matuka Sunana yana cikin wannan Littafin.


ﺳﺌﻞ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺯﻳﻦ ﺍﻟﻌﺎﺑﺪﻳﻦ " ﻉ " ﻋﻦ ﺗﻤﺎﻡ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻘﺎﻝ " :

ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭ ﺁﻝ ﻣِﻦْ


Ma'ana:

🌷An tambayi Imam Zainul Abidina (A.S) game da

cikar Sallah, Sai Imam ya amsa da cewa: Salati

ga Annabi da Iyalan Sa tsarkaka.


🌷Imam Ali (as) yace: "Salati ga Annabi (s) yana bice zunubi

tamkar yadda ruwa ke bishe wuta."(Thawabul

A'amal:186)


🌷Manzon Allah (saw) yace: "Salati gare ni da iyalaina yana gusar da munafunci (daga zuciya)" (Akhlak Wal Aadab:87).


🌷A wani wuri Yana cewa: Wanda yayi min salati guda daya, ko kwayar zarra ba za ta rage a zunuban sa ba." (Bihar:94)


🌷Imam Bakir da Imam Sadik (as) sunce: "Mafi nauyin abin da za a dora a mizanin mutum ranar Alkiyama shine Salati ga (manzon Allah) Muhammad (s) da

iyalan gidansa (as)." (Bihar:71).


🌷Manzon Allah (saw) yace: "Duk inda kuka kasance, to ku yi min salati domin salatin ku yana iske ni."


🌷Manzon Allah (saw) yace: "Ranar Alkiyama zan tsaya a wurin mizani, duk wanda munanan ayyukan sa suka nauyaya akan kyawawa, zan kawo salatin da yayi min ina dorawa akan mizanin sa har sai kyawawan ayyukan sa sunyi rinjaye dashi" (Thawabul A'amal:187)

Comments