Main menu

Pages

SHARI'AR KOTUN KOLI, BUHARI YA SHA KAYE KAN DOKAR ZABE

 


Buhari ya sha kaye a Kotun Koli a shari'a kan dokar zabe ta 2022

Kotun Koli a Najeriya ta yi watsi da karar da Shugaba Muhammadu Buhari da Babban lauyan gwamnati suka shigar, suna bukatar fashin baki kan sashe na 84 na dokar zabe ta 2022 da aka yi wa garambawul.SHARI'A

Sashen ya haramtawa duk wani mai rike da mukami na siyasa, da aka nada a dukkan matakai, ya kada kuri'a a zaben fitar da gwani na duk wata jam'iyya.Alkalan Kotun bakwai da suka yi zaman ranar Juma'a a karkashin jagorancin Mai Shari'a Musa Dattijo, dukansu sun amince cewa karar yunkurin wahalar da kotu ne kawai.A hukuncin da Mai Shari'a Akomaye Agi ya karanto, Kotun Kolin ta ce ba zai yiwu Shugaba Buhari ya nemi a goge sashen na 84 da dokar zabe 2022, bayan da a baya ya aminta da shi.

Comments