Main menu

Pages

MUHIMMAN ABBW 5 DA ATIKU YAYI ALKAWARI IDAN YA DARE KUJERA. MULKI

 



Abubuwa 5 da Atiku yace zai Maida hankali kansu idan yaci zabe

Dan takarar shugaban kasa karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa matakin da za su dauka na gaba a halin yanzu shi ne, yadda za su yi tsarin kamfe na kasa baki daya.


Atiku ya fadi haka ne yayin da yake bayyana sunan Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin wanda zai yi masa mataimakin shugaban kasa a zaɓen 2023.


Atiku ya shaida wa BBC Hausa cewa zai mayar da hankali kan abubuwa biyar idan ya zama shugaban Najeriya:


Sake dawo da hadin kan 'yan Najeriya

Ya ce an samu rarrabuwar kawuna tsakanin kabilun Najeriya, ba wai lokacin zabe kadai ba, yana mai cewa batun shugabanci na daya daga cikin abin da ke haddasa rashin zaman lafiya tsakanin yankunan kasar, tun daga kudanci, arewaci, yammaci da kuma gabashin kasar.


Don haka ne Atiku Abubakar ya ce zai dawo da hadin kan 'yan kasar.


Dawo da zaman lafiya

Babban kalubalen da ake ganin Najeriya ke fuskanta cikin shekarun nan shi ne matsalar tsaro. Kama daga ta da kayar bayan 'yan Boko Haram, da ISWAP, sai kuma matsalar barayin daji da ke sace mutane domin neman kudin fansa.


Da rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma, da 'yan sara-suka, da rikicin kabilanci musamman tsakanin 'yan arewacin Najeriya da kudancin kasar.


Farfado da tattalin arzikin kasa

Tattalin arzikin Najeriya na fuskantar komawa baya a dan tsakanin nan, alkalumma masana tattalin arziki sun nuna a shekarar 2020 an samu koma baya da kusan kashi 4 cikin 100, kuma tun daga wannan lokacin lamarin ke kara tabarbarewa.


Ana danganta hakan da faduwar darajar man fetur a kasuwannin duniya, da barkewar annobar korona da duniya tai fama da ita tun daga shekarar 2020.Tsada rayuwa musamman kayan masarufi da na bukataun yau da kullum na kara jefa 'yan Najeriya cikin halin ni 'ya u.


Tabbatar da an gyara fannin ilimi

Wasu na ganin fannin ilimi a Najeriya ya durkushe tun daga matakin firamare har zuwa jami'a, rashin kayan aiki, da ingantattun malami domin koyarwa, da lalacewar gine-ginen wasu makarantun da korar malamai daga bakin aiki bisa hujjar rashin cancantar koyarwa na ci wa 'yan kasar tuwo a kwarya.


A matakin jami'a kuma yawan yajin aikin malamai kan biyansu hakkokinsu da gwamnati ba ta yi ba, ya janyo yajin aiki a daukacin jami'o'in Najeriya, lamarin da ya janyo tsaikon kammala karatun ga daliban da ke shirin kammala karatun jami'a. Da rashin farawa ga sabbin dalibai.



Sake duba tsarin mulkin Najeriya

Bayan an shafe lokaci mai tsawo ana tafka muhawara, majalisun tarayyar Najeriya biyu sun kaɗa ƙuri'u kan wasu muhimman batutuwan da ake son yi wa gyara domin inganta tsarin mulkin ƙasar.


Cikin watan Maris din shekarar nan ne dai 'yan majalisun suka kada kuri'ar, cikin abubuwan da majalisun tarayyar Najeriya suka kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da bai wa shugabannin majalisar rigar kariya da wasu batutuwa cikin gyaran fuskar da ake shirin yi wa tsarin mulkin kasar.


Bayan kammala zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP, an samu rarrabuwar kawuna tsakanin 'ya'yanta, amma Atiku Abubakar ya ce tuni suka kafa kwamiti na musamman da zai duba wannan matsalar da tabbatar da zman lafiya da hadin kai tsakanin 'ya'yan jam'iyyar PDP.


''Babu yadda za a yi jam'iyya mai tarihi kuma babba kamar PDP a ce an yi zabe ba tare da an samu wata matsala ba, abubuwa ne da ko a zamantakewar iyali ana samun sabani. Muna nan muna kan tuntuba, kuma insha Allahu za mu gyara,'' in ji Atiku Abubakar.


Dukkan jam'iyyun siyasar Najeriyar da suka kammala zabukan fidda wanda zai musu takarar shugaban kasa karkashin tutar jam'iyyun na su, sun ce sun shirya tsaf domin tunkarar zabe mai zuwa.


Masana sha'anin siyasa na ganin, fafatawar za ta yi zafi ne tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da babbar jam'iyyar hamayya ta kasar PDP.

Comments