Main menu

Pages

MAGANIN AMOSANIN KAI, GASHI YAYI KARFI, DA KUMA YADDA ZAI YI TSAWO.

 Gyaran gashi da maganin Dandruff

To a yau mun kawo maku wani hadi dake maganin Dandruff, sannan yasa gashi yayi karfi ya daina karyewa. Da hadin abubuwa biyu kacal Insha Allah.


Magannin dandruff da karyewan gashi

Abinda zakiyi shine, zaki samu tumatur da Sabulun Salo. Sai ki matse ruwan tumatur din kamar Rabin Kofi haka, ki tace wadannan 'ya'yan sai ki dauko Sabulun salonki, ki Saka a ciki har sai ya narke. Idan ya narke sai ki dauko ki zuba a kanki ki caccakuda shi da gashin ki tabbata ko Ina ya samu. 
To daga nan sai ki samu shower cap ko Leda ki daure kan ki kwana dashi. Da safe ki samu ruwan dumi mai dumi sosai ki wanke kan ki shassharce shi da comb. Ki jure yin hakan na tsawon sati biyu. Insha Allah duk Wani cuta ta Kai irin su dandruff da karewan gashi duk zai maganinsu. Domin gashin zaiyi karfi ya daina karairayewa. Dandruff Kuma kunyi bankwana Insha Allah.Gyaran gashi yayi baki yayi tsawo tare da laushi

Idan Kuma kina so kanki yayi tsawo sosai yayi baki da laushi, to ga abinda zakiyi.
Zaki samu man zogale, da busasshen ganyen magarya, da kanunfari Dan kadan.
Zaki daga ganyen magarya da kanunfari yayi laushi sosai, ki tankade. Sai ki dauko wannan man zogale din ki kwaba da wannan Garin magarya da kanunfari ki shafa a kanki Shima ki tabbata ko Ina ya samu. Sai ki barshi tsawon awa daya sannan ki wanke da ruwan dumi. 


Ki juri yin haka lokaci Zuwa lokaci Zaki sha mamaki. Allah Ya bada ikonyi Ameen.

Comments