Main menu

Pages

CIKAKKEN BAYANI WADDA ZATA MAYE GURBIN SUMAYYA A LABARINA SERIES FILM

 


Wadda zata maye gurbin Sumayya a Labarina.

Bisa dukkan alamu, jarumar shirin fim din Alaka, Habiba Aliyu, wacce aka fi sani da Ummi Alaqa ce zata maye gurbin Nafisat Abdullahi a cikin shirin Labarina mai dogon zango.


LabarunHausa ta gano hakan ne bayan bibiyar shafin jarumar wacce ta hada hotonta da na Nafisat Abdullahi inda ta ke tambayar mabiyanta akan wacce rawa za ta taka idan ta maye gurbin Nafisat a shirin fim din. Labarunhausa na ruwaito 

Idan ba a manta ba, shirin ya yi matukar farin jini wanda an kwararo kammala Zango na biyu jarumar suka samu matsala da mashiryin shirin, Naziru Sarkin Waka da kuma darektan shirin, Malam Aminu Saira, daga nan shirin ya tsaya cak.


Related Articles


Matsayin da na ba mahaifina na gida, shi na bai wa Adam Zango -Jaruma Tumba GwaskaSai dai kamar yadda Baban Chinedu ya shaida a wani bidiyo da yayi ana tsaka da rikicin Nafisat da Naziru, ya ce saboda rashin ihsani ne tsakanin mashirya shirin da kuma jaruman ya sanya su ka dakata daga ci gaba. 

Amma a bangaren Nafisa, tun bayan dakatarwarta ta saki wata takarda wacce ta ke baiwa mutane hakuri akan cewa akwai abubuwa masu matukar muhimmanci da suka sha gabanta, wadanda su ne zasu dakileta daga ci gaba da shirin.
A ranar Lahadi, jaruma Ummi ta yi wallafa a shafinta na Instagram bayan ta hada hotonta da na Nafisat Abdullahi, daga nan tace:"Shin wacce irin rawa kuke ganin zan taka a gurbin Sumayya cikin shirin Labarina Series.”

Nan da nan mutane suka bazama suna ta tsokaci karkashin wallafar, wasu suna ganin zata taka babbar rawa, yayin da wasu suke ganin gogewarta bata kai ta maye gurbin Sumayya ba.


 Tsokacin jama’a karkashin wallafar

LabarunHausa ta tattaro wasu daga cikin tsokacin mutane:


t_jega ya ce:


“Ina miki fatan kiyi abinda yafi nata kyau. Allah ya kara daukaka.”


real_ab_yareema ya ce:


“Bisa yadda takardar tazo, shirin bai dace da ke ba. Shekarunki basu kai ba. Kalar fatarku ta zo daya. Duk da cewa an canja fuskarta amma ai ba a canja girman jiki da murya ba. Ya dace ace an yi canjin yadda ya dace.”


tukur_ms ya ce:


“Mu dai masoya shirin Labarina mai dogon zango ne. Allah ya bada sa’a.”


its_young_writer ya ce:


“Abin ma be yi tsari ba. Ke kina karamarki a saki matsayin mai shekaru 30 da doriya.”

Comments