Main menu

Pages

YANDA ZAKAI FREE DIN STORAGE NA WAYARKA DON KARA SAMUN SPACE.

 



Yadda zakai free space na wayarka android ko iphone.


Lokutta da dama zaku ga storage din waya ya cike, har ta kaiga ko photo bata dauka ko a Sanya dan Abu kadan sai tayi ta nuna insufficient storage, Kuma sai ka gama bincike wayar tsab kaga ba wata tsiya ka saka da zai hakan ba. 



To a yau mun kawo maku wasu hanyoyi da zaku bi wajen rage komatsan da ke cikin wayarku don samun Isasshen space.



Amma da farko ya kamata ka fara duba storage na waya kaga space din ya yake MBs nawa ya rage.



Idan kana son gane storage dinka a android ko iphone zaka shiga General setting, sai Kai tapping on storage, to anan zaka ga adadin abinda yayi saura na storage din ka.



Kuma anan ne zaka gane meye ya cinye ma space apps ne ko videos,  ko pictures idan iphone ne akwai Apple Podcasts, wannan yana daukar gigabyte sosai na space.



Za Kai scrolling kasa inda aka rubuta Podcasts zaka iya shiga ka goge dai daikun abubuwa dake ciki ta hanyar yin swipiy dama ko hagu, ko kayi amfani da Edit button wajen gogesu.



Daga nan sai ka koma wajen photos, kafin ka fara yin komai ka sani cewa idan kana amfani da iCoud, to fa duk abinda ka goge a cikin wayarka ta iphone to har na cikin icloud din ma ya goge, wannan app din dake cikin wayar kamar shine madubin icloud storage din ka.




Don haka da kaje kana deleting abubuwa manually, yafi kawai kaje cikin iphone dinka ka shiga settings, ka shiga Apple ID, ka shiga icloud, sai ka shiga photos, amma ka tabbatar wajen photos din Optimize iphone storage is toggled on. Shikenan iphone dinka zatai managing storage automatically ka samu space a wayarka.




Sannan hanya mafi sauki na da zakai free space shine na amfani da wani app da ake cema "Gemini photos". Da kayi downloading dinsa zai ringa scanning photos dinka Yana sorting dinsu yayi categorizing dinsu wajen taimakawa da samun duplicate na kowane photo da screenshot da sauran abubuwa. 



To sai dai Kuma wannan app na kudi ne, $5 per month ko Kuma $20 a shekara.


Ina fatan wannan Dan bayani zai amfanar sai mun hadu a darasi na gaba.

Comments