Main menu

Pages

YADDA A KA KASHE 'YAR JARIDAR ALJAZEERA DA TAKAITACCEN TARIHIN TA

 


Tarihin Yar Jarida Shireen Abu Aqla

Miliyoyin mutane sun san Shireen Abu Aqla saboda rahotanninta kan rikicin Isra'ila da Falasɗinawa


An kashe shahararriyar mai aiko da rahotanni Shireen Abu Aqla wadda 'yar Falasɗinu ce mai shaidar zama 'yar Amurka yayin da take tsaka da turo wa gidan talabijin na Aljazeera rahoto a gaɓar yamma da Kogin Jordan wato West Bank da Isra'ila ta mamaye.


Aljazeera da ke Qatar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa dakarun Isra'ila sun kashe wakiliyar tata "da gangan" kuma "ba tare da wani haƙƙi ba".


Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta ce an kashe Abu Aqla bayan an ji mata mummunan rauni a ka a lokacin da take haɗa rahoto kan samamen da dakarun Isra'ila suka kai kan wani sansani 'yan gudun hijira a Jenin da safiyar Laraba.


Sanarwar ta ambato wani da lamarin ya faru a kan idonsa na cewa "soja mai harbi daga nesa ne ya harbe ta a ka, duk da cewa tana sanye da hular kwano da rigar da ke bayyana kalmar 'jarida' ƙarara".


Firaministan Isra'ila ya ce "akwai yiwuwar" 'yan bindigar Falasɗinu ne suka kashe ta lokacin da suke musayar wuta.


Wace ce Shireen Abu Aql

An haifi Shireen Abu Aqla a Janairun 1971 a Birnin Ƙudus. Ta kammala Sakandaren Rosary Sisters da ke unguwar Beit Hanina ta Ƙudus


Tun farko ta karanta fannin zane a jami'ar Jordan University of Science and Technolog


Sai kuma ta samu shaidar digiri kan yaɗa labarai a jami'ar Yarmouk University da ke Jordan, inda ta ƙware a ɓangaren rubutattun labarai


Bayan ta gama digiri, Shireen ta yi aiki da gidajen jarida da yawa tun daga cikin Falasɗinu, ciki har da rediyon Voice of Palestine, da Amman T


Ta koma Aljazeera a 1997 shekara ɗaya bayan kafa ta kuma ta zama ɗaya daga cikin masu aiko da rahotanni na farko a tasha


Falasɗinawa masu zanga-zanga riƙe da hotunan Shireen Abu AqlaAbu Aqla ta shahara cikin shekara 25 da suka gabata sakamakon rahotanninta kan batutuwa da dama a rikicin Isra'ila da Falasɗinawa.


Daga ciki akwai Boren Falasɗinawa na shekarar 2000 (Palestinian Intifada), da afka wa sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da Tol Karam a 2002.


Kazalika, ta yi rahotanni kan hare-haren Isra'ila a zin Gaza.


Shireen ce 'yar jarida Balarabiya ta farko da aka ba wa damar shiga gidan yari na Ashkelon da ke kusa da Gaza a 2005.


Ta haɗu da fursunoni Falasɗinawa da Isra'ila ta ɗaure tsawon shekaru.


Abu Aqla ziyarar da ta kai bursin ɗin na ci gaba da zama a ƙwaƙwalwarta saboda yadda ta ga yanayin da Falasɗinawa ke ciki da idonta.


Cikin wata hira da ta yi da Aljazeera a baya, Abu Aqla ta ce dakarun Isra'ila sun sha zargin ta da yin rahotanni daga fagen yaƙi sau da yawa.


Ta ƙara da cewa a kodayaushe tana jin cewa ana haƙonta sannan kodayaushe tana rigima da dakaru 'yan kama-wuri-zauna.


Cikin wani bidiyon talla da Aljazeera ta wallafa a Oktoban 2021 na cika shekara 25 da kafa ta, Abu Aqla ta ce: "Na zaɓi aikin jarida ne don na kasance kusa da mutane.


Ba lallai ya zama abu mai sauƙi ba gare ni wajen sauya abubuwan da ke faruwa, amma aƙalla na samu damar faɗa wa duniya halin da suke ciki...Ni ce Abu Aqla."

Comments