Main menu

Pages

HADIN SABULAI KALA KALA DON GYARAN JIKI




GYARAN FATA DA JIKI HADIN SABILU

dole maigida ko saurayi yai tabinki zai-zai to yaga kin yi kyau.

ke dai yi wanka da

SABULUN BITA ZAI-ZAI

• Dudu osun

• Dettol

• Sabulun Ghana

• Garin zogale

• Farar albasa

sai Ku hade su guri daya Ku kirba su a turmi ki mulmula Ku rinka wanke fuska zaku ga yadda fuskarku zata yi kyau.



BITA ZAI-ZAI

sunan hadin kenan idan dai kana yin wannan hadin zaki sha mamaki za kibani labarin amfani hadin tabbas idan amarya tayi wannan hadin zata kidima ango har yakasa gane ta sai yayi da gaske ke dai yi mugani domin gyaran jiki.

• Ayaba

• Lemon tsami

• Tataciyar madara

• Kwai uku

zaku sami ayaba mai kyau Ku bare Ku matse da hannun ko Ku markada yi laushi sai Ku zuba tataciyar madara Ku fasa kwai kamar uku amma farin zaku zuba sai Ku matse lemon tsami Ku gauraya shi Ku shafa a jikin Ku ya sami kamar tsayin ¹ daya sai kuyi wanka da ruwan zafi, idan har kuka lazimci yin haka ba magana.




SABULUN GYARA FATA

idan har kina San gyaran fata kina iya wannan hadin domin gyaran jiki, fatar ki zata yi kyau sossai.

• Sabulun sel

• Sabulun salo

• Lalle

• Zuma

• Garin darbejiya

• Sabulun premier

• Kurkum

• Sabulun zaitun

• Dudu osun.

• Dettol

Zaki daka sabulun duka ki zuba a mazu Bi ki zuba lalle da majigi a Kai da zuma da kur-kur ki juya shi sossai garin darbejiya kuma ganyen Zaki samun ki shanya ki daka ki tankade ki hada akan sabulun ki saka ruwa kadan ki juya yadda zai hade jikinsa Zaki ga yadda fatarki zata canja sirrin kyau.



 HADIN GYARAN JIKINMU TA KO INA

idan kina yin haka dole maigida yaga kinyi kyau fiye da ko yaushe jikinki da fatar fuskar ki zata yi haske.

• Lalle

• Kwanduwar kwai ³

• Manja cokali ³

• Kur-kur

sai ki kwaba su guri daya Ku shafe jikinku zuwa awa guda, sai Ku yi wanka da ruwa zalla in dai kyan fata ne sai dai agani a jikinku, kowa zaiyi sha'awar ki.



SABULUN KURAJE

• Asef soap

• Pharmaderlm soap

• Kanwa

• Jar dilka

• Zuma

• Lemon tsami

Ki goga sabulun kowanne guda uku, sannan ki zuba kanwarki dakakkiya cikin karamin cokali, kinkwaba dilka da ruwan zafi cikin cokali cin abinci daya ki zuba a ciki, ki matse lemon tsami daya a Kai kisa Zuma cokali biyar ki hada ki kwaba sosai, ki lailaya sai ki dinga shafawa a fuskarki kamar ya rage minti biyar kafin ki shiga wanka, Indan kin shiga wanka sai ki kuma wanke fuskarki da sabulun kamar uku ko Dama da haka.



SABULUN FIDDA TABO

ko Zuma Zaki Iya shafawa idan Zaki kwanta bacci sai da safe ki wanke da ruwan dumi.

• Misscoroline soap

• Shary soap

• Aloevera soap

• Garin alkama

• Zuma

 • Kanwa kadan

• Lemon tsami rabi 1/1

Sai ki goga su ki hada ki zuba Zuma a ciki da lemon tsami da kanwarki ki kwaba, ki dinga shafawa fuskarki minti biyar kafin ki shiga wanka, idan kuma zakiyi wanka dashi Zaki dinga wanke fuskarki.

Comments