Main menu

Pages

IN HAR KANA AMFANI DA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN CODES DIN A MATSAYIN ATM PIN TO KAYI GAGGAWAR CANZAWA

 



Scam Alert: Idan kana amfani da wasu daga cikin wadannan 12 codes a matsayin ATM pin dinka to kayi gaggawar canzawar.


Akwai wasu codes da in kana amfani dasu a matsayin password to yanzu 'yan damfara na iya amfani dasu wajen gano komai naka na account.


Abinda yasa ake iya hacking bankuna a yau shine saboda amfani da wasu weak codes da Kuma ake amfani da su a matsayin password.



Kamar yadda kowa ya sani ne idan babu wadannan pin guda hudu ba zaka iya transfer na kudi ba, ko fiddo kudin, ko wani abu Mai muhimmanci da zakayi a account dinka ta fannin transactions. To a shawarce shine kayi amfani da pin ko password mai karfi sosai don kar ka zamto cikin wadanda abin zai shafa.



A yau za mu kawo maku ko nuna maku wasu codes a kalla guda 12 da kar ka kuskura kayi amfani dasu a matsayin password.



Wadannan sune codes din da za a kiyaye;

1- Kar ka sake kayi amfani da Shekara a matsayin pin. Misali

1999,. 2003,. 2020, 1887.



2 - Kar kayi amfani da number daga kasa abin da yayi sama Misali

1234,. 7890,. 4567,. 9876



3 - Kar kayi amfani da number iri daya. Misali

5555, 9999,. 7777, 1111


Muna fatan wannan post zai taimaka wajen ganar daku don ku gyara ku kiyaye kuma. Idan kana/kina amfani da daya daga cikin wadannan codes ko ire irensu to yi maza maza ku canza.

Comments