Main menu

Pages

ABUBUWAN DA YA KMT AMARYAR GOBE TAYI (1)Abubuwan da ya kamata Yarinyar da Za a yima Aure ta fara yi kafin Biki. Kashi - Kashi har Kashi 4


Ana son amaryar gobe ta fara wannan shirin tun ana bikinta saura watanni uku.


MATAKAI

Ana son amaryar gobe ta fara da gyaran gabanta TOILET INFECTION.

Wata cuta ce da take samun mace da namiji, cuta ce wadda take a cikin mace da kuma gaban ta. Cuta ce wadda wani zai iya daukar ta daga wani, za'a iya daukar ta idan wata tayi fitsari a daidai wani wuri kema sai kije kiyi, za kuma ki iya daukar ta ta hanyar sharing pants da wadda take dashi. Haka kuma ana iya daukar shi a yayin saduwa (sex), mace zata iya gogawa namiji haka namijin ma zai iya gogawa mace shi.


      Idan aka kasa mata kashi dari to fa 95% suna da wannan cutar. Cuta ce mai matukar wahalar magani ga wanda basu san yanda zasu magance shiba.

ABUBUWAN DA TOILET INFECTION YAKE HAIFARWA

1- rashin gamsar wa a yayin jima'i

2- rashin haihuwa

3- rikicewar al'adah

4- soshe-soshen gaba a cikin mutane, har wasu su ringa k'yamar Mutum

5- fitar farin ruwa

6- gaba ya ringa yin zafi a yayin yin fitsari

7- jin tsirar gaba ba tare da dalili ba

8- yin fitsari guntu-guntu.HANYOYIN MAGANCE TOILET INFECTION

1- Ki daina inserting ko wane irin magani a gaban ki, sai miski, duk wata kawa ko yar uwarki da zata baki wata shawara akan ki matsa wani abu yana karin ni'imah kar kiyi wallahi, ki bata shawara itama tayi kokarin dainawa.

2- ki ringa tsarki da warm water, (not too hot water dan kar ya sale ki)

3- ki ringa inserting da miski a koda yaushe, yana warkar da wannan cutar sosai.


Allah Ya sa a amfanar, post na gaba za a dora da cigaban abubuwan da ya kmt amaryar gobe tayi kafin lokacin Biki.

Comments