Main menu

Pages

ABUBUWAN DA YA KAMATA AMARYAR GOBE TA YI KAFIN BIKI (2)

 Shirye - Shiryen Amaryar gobe kafin Biki Kashi na biyu (2)


Ana son amaryar gobe ta fara wannan shirin tun ana bikinta saura watanni uku

SAI KUMA GYARAN NONO

Nono wani bangare ne mai matukar muhimmanci a jikin 'ya mace domin shine cikon matantakarta ko a cikin yan uwanta mata bare a wurin mijinta da bai da shi dole ne mace ta kula dashi.

❊ Mata ba ko wanne namiji yake son manya breast ba.


❊ Haka ba ko wanne namiji yakeso kananan breast ba.

To koma dai yaya ne, manya gareki ko qanana to kiyi kokari kiga cewa kina kula dasu kar ki bari su zube kamar silifas, most especially ga masu manya. A ringa harhada abubuwan da zasu Santa su ciko su tsaya qyam ba tare da sun russina ba.


Akwai abubuwan da zaki a sha kamar Kun alkama da Farar shinkafa, Sabaya, Shafa Hulba da Sauran natural abubuwa but kar ki sake Kisha maganin warin girman breast na kanti.


Sannan kuma a kiyaye yin daurin kirji, daurin kirji shine wanda mata ke yi a kullum idan sun fito daga wanka, in dai haka ne ma'anarsa ashe to bai kamata ya fi minti 5 a kirjin mace ba, domin yana da illoli kamar haka; sa nonon mace ya zube da sauri ya zama tamkar silifas. ciwon kirji saboda danne jijiyoyi hanyar jinin da suke biyowa ta saman nononta data tamke qashin kirji. Sannan a daina kwanciya rub da ciki Shima yana zubar da breast sosai, don haka sai a kiyaye.


Sai mun hadu a post na uku akan irin shirye shiryen da Amarya ya kamata ta fara kafin Biki.


Comments