Main menu

Pages

YADDA AKE HADA LEMUN KWAKWA DA ABARBA.Lemon Kwakwa Da Abarba

Kayan Hadi

1.Kwakwa

2.Abarba 

 3.Lemon zaƙi

4.Sugar

5.Flavour 


Yadda Zaki hada

Za ki goge kwakwa da abun goga kubewa, ki markaɗa a blender sai ki zuba ruwan sanyi a tace da rariya sannan ki markada abarba ko (lemon zaki) ki tace ta ki zuba a kwano, sannan ki dafa suger da ruwa ki barshi ya huce.


Sai ki haɗa kwakwa da abarba a guri daya ko lemun za ki zuba suger da flavour ki juya sosai sai kisa a fridge yayi sanyi.


wannan lemon ana haɗashi ne lokacin da za’a sha, idan kuma aka haɗa aka sa shi a frigde za kiga man kwakwar ya taso, to ba lalace wa yayi ba sai akara markadawa.

Comments