Main menu

Pages

KO KINSAN AMFANIN RUWAN LALLE GA FATARKI

 Amfanin Ruwan Lalle a Fata

Jama’a da dama sun san cewa lalle abin ado ne ga mace. Bayan haka ruwan lallen ma na da matukar amfani ga fata. Ana shuka lalle ne a wuraren da ke da zafi. Yanayin zafin wuri ke nuna kyan launin lalle. Don haka a yau na kawo muku yadda za a yi amfani da lalle a fata.


Domin samun sulbin fuska, a jika lalle na tsawon awa biyu sannan a kwaba shi da ruwansa sai a diga man zaitun da kwanduwar kwai sannan a shafa a fuska na tsawon minti talatin sannan a wanke da ruwa. Ana son shafa irin wannan hadi kamar sau daya a mako.


A jika lalle da ruwa sannan a zuba man zaitun da man kwakwa a rika wanke gashin kai da shi domin hana gashi tsinkewa da kuma sanya gashi laushi,


Domin magance amosanin kai; a kwaba lalle da ruwan lemun tsami kadan sannan a shafa a fatar kai a bar shi na tsawon minti goma zuwa sha biyar kafin a wanke da sabulun wanke gashi.


Ruwan lalle shi ne babban abin da ke taya lalle kamawa a fatar hannu. Ana gane lalle mai kyau ne ta ganin irin launin ruwan da ke jikin lalle.


Shi kansa lalle abin ado ne ga mata idan aka sanya shi a tafin kafa ko a hannu.

Ana wanka da ruwan lalle bayan ya tsumu domin kara launi ga amaryar gobe. Za a iya jika ruwan da lalle mai dan dama ya tsumu bayan amaryar gobe ta gama wanka za ta iya watsa wannan ruwan a wankan karshe domin sanya fata laushi da launi mai kyau.

 

Comments