Main menu

Pages

WANI ATTAJIRI ZAI SAYE TWITTER AKAN DOLLAR BILLION 40



 Elon Musk: Mai kuɗin duniya ya yi tayin sayen Twitter kacokan

Shugaban kamfanin ƙera motoci na Tesla kuma attajirin duniya, Elon Musk, ya yi tayin sayen dandalin sada zumunta na Twitter kacokam don ya "fito da" da baiwa ta musamman da kamfanin ke da ita.


Cikin wata sanarwa ta ban-mamaki, Mista Musk ya ce zai biya dala 54.20 kan kowane hannun jari ɗaya, inda ya yi hasashen darajar dandalin kan dala biliyan 40.


A kwanan ne aka ruwaito cewa Musk ya zama mai mafi girman hannun jari a Twitter bayan ya ƙara yawan hannun jarinsa a kamfanin.


Ya ƙara da cewa idan ba a karɓi tayin da ya yi ba: "Zan yi tunanin sauya matsayina na mafi yawan hannun jari."


Wasu bayanai da ya miƙa wa hukumar kula da harkokin kuɗi ta Amurka sun nuna saƙonnin da Musk ya tura wa majalisar zaɓaɓɓu na Twitter cewa ya yanke shawara a ƙarshen mako cewa ya kamata kasuwancin kamfanin ya zama mai zaman kansa.


An gayyaci Mista Musk ya kasance cikin majalisar zaɓaɓɓun kamfanin amma Twitter ya sanar ranar Lahadi cewa ya janye tayin da ya yi masa.


Cikin bayanan, Musk ya ce ba ya son "je-ka-ka-dawo" sannan ya ce: "Tayi ne mai tsoka kuma masu hannun jarinku za su so shi."


Zai ɗauki matakin sayar da hannun jarinsa na Twitter idan har ba a karɓi tayin nasa ba, a cewarsa.


"Wannan ba barazana ba ce, kawai dai ba zai zama zuba jari kai waye ba idan ba a samu sauyin da ake buƙata ba," in ji shi.

Comments