Main menu

Pages

TABDI!! AN QARA KUDIN DSTV DA GOTV

 Yan Najeriya da dama sun nuna fushinsu a shafukan sada zumunta kan sanarwar karin kudin amfani da DSTV da GOTV da kamfanin talabijin na Multichoice na tauraron dan Adam ta yi.

A ranar Talata ce kamfanin multichoice ya fitar da sanarwa kan sabbin kuɗaɗen da kwastomominsu za su biya a matakai daban-daban.


Kamfanin ya ce daga ranar 1 ga watan Afrilu, mutanen da ke amfani da nau'rar decodarsu wajen kallo za su biya N21,000 maimakon N18,400 a matakin kololuwa na premium.


Sannan masu amfani da GOTV a matakin kololuwa na max na N3,600 za su koma biyan N4,150.

Wannan sauyi ko karin ya zo wa 'yan kasar da dama da bazata musamman a wannan lokaci da 'yan Najeriya ke kuka da hauhawar farashi da tsadar rayuwa.


Mutanan da ke kokawa na tsokaci kan da wane za su ji a wannan rayuwa da komai ke kara kudi na walwala, baya ga koken sufuri da tsadar abinci da rashin man fetur.

Shi dai kamfanin Multichoice ya kare matsayarsa na wannan karin kudi kan yanayin kasuwanci a kasar da tsadar kayayyaki wanda ya ce su suka haddasa wannan sauya farashi nasa.


Galibin 'yan ƙasar nan na tsokaci ne a shafukan sada zumunta irinsu Twitta da kuma kwatanta kudaden da suke biya da yawan tashoshin da ake ba su.

Sannan suna duba zabin da ya rage a garesu ko ci gaba da amfanin da kamfanin ko sauyawa zuwa ga mai sauki.

Wasu kuma na kiran a kauracewa amfanin da Multichoice baki daya suna cewa akwai wasu hanyoyi ko kamfanonin da ake iya rungumar tsarinsu mai sauki.

To Allah Ya kyauta Ya kawo mana sauqi ta kowacce fuska. Ameen

Comments