Main menu

Pages

IKON ALLAH!! MATAR DAKE DA AL'AURA BIYU, MAHAIFA BIYU

 Matar da ke da farji biyu da mahaifa biyu.

Elizabeth Amoaa ta umarci mata su daina shiru idan suna cikin yanayi na azaba


"Sunana Elizabeth Amoaa - matar da ke da mahaifa biyu, da al'aura biyu ta ciki da ta waje," kamar yada matar mai shekara 38 'yar Ghana ta Fada.


Muryarta na rawa cikin yanayi na tausayi lokacin da take ba da labarin irin wahalar da ta sha saboda wannan matsala ta lafiya da ba a saba gani ba.


Likitoci ba su iya fahimtar ainihin me ke damunta ba har sai da ta kai shekara 32 a duniya.


Mazauniyar Birtaiya a yanzu, Ms Amoaa ta ce ta shafe tsawon shekaru tana fama da matsalolin matsanancin ciwon ciki da ke hana ta wasu ayyuka kafin a gane cewa tana dauke da komai biyu-biyu ne a ɓangaren farjinta da kuma mahaifa, yanayin da ba a saba samun irinsa ba.


Har ta yi ciki, kuma ta haifi jaririya mace da ba ta kai watannin haihuwa ba a 2010 ba tare da an fahimci me ke damunta ba.


Tana ganin jinin haila lokacin da take dauke da juna biyu yayin da ɗan tayin da ke jikinta ke girma a mahaifarta ta hannun dama da ke da lafiya.


"Ina iya daukar ciki a mahaifata da ke dama, sanan kuma na ci gaba da ganin jinin haila a mahaifata da ke hagu.


Wannan ne ya sa lokacin da nake dauke da cikin diyata ina ganin jini," kamar yadda ta shaidawa wakilinmu.


Bayan tiyatar da aka ma ta sau da dama, da daukar hoton cikinta da magunguna, yanzu ta fahimci abin da ke damun jikinta tun a 2015.


Ms Amoaa yanzu na son duniya ta san irin akubar da ta tsinci kanta a ciki, saboda kar saura mata su gamu da irin wannan wahala a gaba.


Ta fuskanci suka lokacin da ta soma fitowa gaban mutane a wani shirin talabijin Ghana tana sanar da su abin da ke damunta, amma wannan bai sa ta karaya ba, domin ba ta da buri sama da ilimantar da mutane.


Ta kafa wata gidauniya da ake kira "Speciallady Awareness" domin wayar da kawuna, hakan nan kuma ta rubata littafi da aka kaddamar a watan Nuwamban bara, kan rayuwarta.


"Shawarata ga mata da ke fama da irin wannan matsala ita ce: kar ku yi shiru; kar ku wahala saboda bakinku a rufe; ku je asibiti domin a duba ku da kyau da ba ku maguguna da kulawar da ta dace, kuna da muhimmanci", kamar yadda ta shaida wa BBC.


Comments