Main menu

Pages
Ladubban Da ake Bi Wajen Addu'a

 Akwai ladubba da ake neman duk mai son Allah ﷻ ya amsa masa addu’arsa ya gabatar da su a yayin addu'ar da gabaninta da kuma bayanta. Su ne: 


 Ana son mai addu'a ya fuskanci Allah ﷻ da kyakkyawar niyyah mai tsarki, ya sakankance cewa Allah ﷻ ne kaɗai zai iya biya masa wannan buƙatun nasa shi kaɗai, don haka wajibi ne ya halarto faɗin Allah ﷻ inda yake cewa: 

﴿ادْعُوا رَبَّكُمْ تَضَرُّعًا وَخُفْیَةً إِنَّهُ لاَیُحِبُّ الْمُعْتَدِینَ۝﴾ () 

Ma’ana: “Ku roƙi Allah ﷻ Ubangijinku kuna masu ƙanƙan da kai da bayyanar da tsoron Allah ﷻ da karyewar zuciya da mai da al'amari zuwa gare Shi a cikin zuciya, domin Allah ﷻ ba ya son masu ta’addanci da ƙetare iyaka.” 


An karɓo daga Mua'zu Ɗan Jabal رضي الله عنه ya ce, yayin da Ma’aiki ﷺ ya aike ni ƙasar yaman sai nace da shi, ka yi min wasiyya ya Ma’aikin Allah ﷺ, sai ya ce, 

))أَخْلِصْ دِینَكَ یَكْفِیكَ الْعَمَلُ الْقَلِیلُ)) الحدیث أخرجه الحاكم وقال: صحیح الإسناد.

Ma’ana: “Ka tsarkake ibadarka ka nufaci Allah ﷻ da ita, idan ka yi haka aiki kaɗan sai ya wadatar da kai a wajen Allah ﷻ.” ()​

Comments