Main menu

Pages

KO KIN SAN AMFANIN SHAFA RUWAN GISHIRI A FUSKA?

 


Amfanin Ruwan Gishiri A Fuska

Ruwan gishiri daman kowa ya san yana tsotse duk wata bacteria dake jikin fata. Sannan tana tightens wato tsuke fata ta rage girman kofofin dake jikin fata, sannan Yana tsotso duk wani mai - mai mara amfani. Sannan yana taimakawa wajen goge fata ta ringa glowing.



Gishiri na taimakawa sosai wajen goge maikon fuska, da duk wani dattin fuska da cire annakiya da kuraje da spot.



Ki gwada hada cokali guda na gishiri cikin ruwan dumi, ki zuba a 'yar roba ko ta turare yadda Zaki ringa fesawa a fuska. Idan kika zuba gishirin ki tabbatar ya narke, sai ki ringa fesawa a fuskarki bayan kin wanke da sabulu. Ki kiyaye kar ya shiga cikin Ido. Ki ringa shafawa kullum.


Ruwan gishiri shine mafi qarfin maganin face acne, yana aiki sosai wajen goge fatar fuska, sannan yana rage bacteria ya kuma mayar da cells na fata zuwa pH level yadda ya kamata.



Sai dai Kuma da za a samu ruwan gishiri wanda yake daga teku to shine mafi amfani fiye da wanda za a hada da, saboda shine ainahin ruwan gishiri mai kunshe da sinadarai da yawa a ciki.



Ruwan gishiri yana tsane fata tare da zame mata kamar antiseptic - properties, wannan ne yasa idan kana da 'yar yanka haka a jiki kaje kayi swimming a cikin kogi indai mai ruwan gishiri ne to zai qame, ya warke dan danan.



Yadda wasu suka ruwaito shine ruwan gishiri, kamar antiseptic ne na duk wasu matsaloli na fata ba kamar fuska ma duk wani acne, pimples, dark spot, blamishes na Fuska duk yana magani.



Ki wanke fuskarki kamar yadda kika Saba da sabulu ko cleanser, sai ki wanke ta sosai da warm water, (ruwan dumi) ki tsane da towel, sannan ki shafa ruwan gishirin.



Magnesium, calcium, potassium da ake samu cikin tekun gishiri duk wadan nan zamu iya kiransu abokan fata ne saboda suna gyara ta.

Wadannan sinadaran suna da Matukar amfani don suna magance duk wata qwayar cutar bacteria dake jikin fata Kuma yana sa rauni yayi saurin warkewa. Allah Ya sa mu dace.

Comments