Main menu

Pages

HANYOYIN DA ZA ABI DON MURJEWAN JIKI BULBUL BA TARE DA AN SHA MGNI BA

 



HANYOYI INGANTATTU NA YIN KIBAR JIKI BASAI ANSHA MAGANI BA.

Wanda duk yakeso yai kiba ya Ganshi mulmul ko bulbul to Dora kanshi akan wadannan Hanyoyin


1- Isasshen Hutu, Mutum ya zamana Yana samun Hutu, rage aiki Mai wahala Wanda yake girgida jikin ta ko Ina.


2- Kwanciyar hankali, Mutun ya nemawa kansa kwanciyar hankali da natsuwa, duk wata harka ko harkalla dake tada hankali Mutun ya kauce Mata, tunane tunane, hange hange da dora ma rayuwa wani guri na daga cikin ababen da suke sa jiki ya tsuke, ga mutum na cin Abinci Amma baya kiba.


3- Anfani da wasu Rikunnen kayan abinci fiye da Wasu, Daga cikin kayan abinci da suke saurin sa kiba da tunbi akwai Yawan cin kayan ciki, Naman tsuntsaye ire iren su Talo Talo, Zabo, da Dakwalen kaji fiye da Jan nama, 


4- Anfani da Vitamins da kuma Carbohydrates, bawa wadannan Rikunnen kayan abinci ko kayan abinci Masu dauke da wadannan sanadaran Gina jiki na taka mahimmiyar rawa wajen Mai da mutum dukeke.


5- Yawan Cin abinci, Mutum ya zama baida aiki sai ci, Da dama Zaman Mutum busy ko wane lokaci na haifar da Rashin cin wadataccen abinci Wanda jiki ke bukata.


6- Kula da wasu Cutuka ajiki, Akwai Dinbin matsalolin da Suke Hana karuwar jiki a sirrince Mutum Yana da matsala Amma Rashin zuwa ayi bincike yasa ayita ramewa Ana lalacewa.


7- Dabi'u, Akwai Dumbin matsaloli da Dabi'u ke haifar wa daga ciki akwai Rashin kiba kamar Anfani da miyagun Kwayoyi, shaye Shaye da Sauran su duka Suna taka mahimmiyar rawa wajen Rashin kiba ta Jiki. Allah yasa mu Dace muyi aiki da Abun.


Ai malam ko Hajiya zakuyi anfani da wadannan matakan Babu wani wahalar Shan magani.


Comments