Main menu

Pages

WAI DAMA HAKA GANYEN KUKA KE DA MATUKAR AMFANI

 


AMFANIN GANYEN BISHIYAR KUKA A JIKIN DAN ADAM:

Ganyen kuka wanda a Ingilishi suke kiransa da (baobab) na dauke da sinadarai da dama wadanda ke inganta lafiyar jiki.


Ga sinadaran da ganyar bishiyar kuka ke dauke da su:


- Vitamin C

- calcium

- phosphorus

- carbohydrates

- fiber

- potassium

- protein

- lipids

- magnesium

- zinc

- sodium

- iron

- lysine

- thiamine


Yana inganta lafiya ta hanyoyi da dama, haka kuma yana magance matsaloli iri-iri da ka iya samun mutum na yau da kullum. Ga kadan daga cikin


Ga kadan daga cikin amfanin da ganyen kukar ke da shi:


1- Yana magance tari da taruwar majina a kirji.

2- Yana rage yawan zufa kamar yadda su turarukan zamani ke yi.

3- Yana rage ciwon Asthma da na koda da na madaciya.

4- Yana rage gajiya da kumburi.

5- Yana rage radadin cizon kwari.

6- Yana magance tsutsar ciki.


Bayan wadannan wata bincike ta nuna ganyar kuka tana da wassu amfanin kamar haka:


- Zazzabin maleriya

- Tarin fuka TB

- Tana ingana garkuwar jiki

- Tana ƙara jini a jiki

- Tana maganin gudawa

- Tana maganin hakori

- Tana maganin ulsa

- Tana rage ƙiba


Sai dai kuma busar da ganyen kuka a rana kamar yadda muke yi na rage masa sinadarai da a kalla kaso 50 cikin dari. An fi son a busar a inuwa.


Lafiya Uwar Jiki

Comments